Kowace Rana da Matsalolinta
Ka Saukar:
1. Na gaskata alkawuran, da Allah ya yi,
Babu abin da zai hana alkawuran cika.
Amma a wasu lokuta,
Nakan yi baƙin ciki fa
Kamar ba mai taimako na, domin damuwoyina.
Amma Allah yana nan.
(AMSHI)
Zan yi addu’a, ga Allah.
A lokacin damuwata
Zai ban ƙarfi in jimre.
Allah na nan; a koyaushe.
Ya ban Kalmarsa Baibul
Da abokan kirki ma.
Kowace rana da wahalarta
Ba na damuwa don gobe
Don Jehobah zai taimaka min.
Sai farin ciki
Ba na damuwa.
2. Bi shawarata ’yan’uwa
Da nake ƙauna.
Ji daɗin rayuwarku,
Manta damuwoyinku.
Allah yana ƙaunarku.
Ya aiko Ɗansa dominku.
Ku riƙa dogara ga shi.
Zai kula da ku kullum.
Kada ku ji tsoro.
(AMSHI)
Yi addu’a, ga Allah
A lokacin damuwarmu
Zai sa mu iya jimre.
Allah na nan; a koyaushe.
Shi ya ba mu Kalmarsa
Da abokan kirki ma.
Kowace rana da wahalarta
Ba ma damuwa don gobe
Don Jehobah zai taimake mu.
Sai farin ciki
Ba ma damuwa.
(AMSHI)
Yi addu’a, ga Allah
A lokacin damuwarmu
Zai sa mu iya jimre.
Allah na nan; a koyaushe.
Shi ya ba mu Kalmarsa
Da abokan kirki ma.
Kowace rana da wahalarta
Ba ma damuwa don gobe
Don Jehobah zai taimake mu.
Sai farin ciki
Ba ma damuwa.