Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Zama da Tabbaci

Ku Zama da Tabbaci

Ka Saukar:

  1. 1. Kuna addu’a.

    Kuna wa’azi.

    Kuna da aminci a kullum.

    Ko da yake ba ma ganin wahalar,

    Amma Jehobah yana gani.

    (KAFIN AMSHI)

    Idan an kai ku gaban hukuma,

    Allah na gani.

    Mu ma za mu bi misalinku

    Muna bayanku.

    (AMSHI)

    ‘Ni na tabbata

    Ba mutuwa ko gwamnati da zai raba mu da Allah.’

    ‘Ni na tabbata

    Ba wani abu da zai iya raba mu da Allah.’

    Sai ku tabbata.

    Allah na kaunar ku.

  2. 2. Kuna ibada

    Kuna jimrewa.

    Kuna dogara ga Allah kullum.

    Suna kokarin hana yin wa’azi,

    Magoya bayanmu sun fi su.

    (KAFIN AMSHI)

    Idan an kai ku gaban hukuma,

    Allah na gani.

    Mu ma za mu bi misalinku

    Muna bayanku.

    (AMSHI)

    ‘Ni na tabbata

    Ba mutuwa ko gwamnati da zai raba mu da Allah.’

    ‘Ni na tabbata

    Ba wani abu da zai iya raba mu da Allah.’

    Sai ku tabbata.

    Allah na kaunar ku.

    Gaskiya ne.

  3. 3. Baibul ya ce: ‘Domin kuna koyi da Allah,

    Za ku sha wuya.

    ‘Duk da wahalarku, kuna ta yin nasara sosai’​—⁠

    Nasara sosai.