Na Dogara da Kai
Ka Saukar:
1. Allah na rike Kalmarka,
Cikin zuciyata
Tana sa in kasance da kwanciyar hankali.
Ko da me za ya faru,
Kalmarka da na sani,
Za ta sa in zama da hikima kullum don
(KAFIN AMSHI)
Kada; in ji tsoro.
In rika bin dokokinka.
(AMSHI)
Kalmarka na, taimaka
Min in jimre a kullum.
A koyaushe ni zan rika dogara da kai.
2. In na fuskanci jaraba,
Da zai sa ni zunubi,
Zan nemi taimako a gun ka Jehobah.
Kuma in yi bimbini.
Don in gane Kalmarka
Kuma ta rika kāre ni, a kullum don
(KAFIN AMSHI)
Kada; in ji tsoro.
In rika bin dokokinka.
Kada na rika yin damuwa.
Domin na san kana kauna ta.
(AMSHI)
Kalmarka na, taimaka
Min in jimre a kullum.
A koyaushe ni zan rika dogara da kai—
da kai.
(KAFIN AMSHI)
Kada; in ji tsoro.
In rika bin dokokinka.
Kada na rika yin damuwa.
Domin na san kana kauna ta.
(AMSHI)
Kalmarka na, taimaka
Min in jimre a kullum.
A koyaushe ni zan rika dogara da kai.