Yi Karfin Zuciya
Ka Saukar:
1. Da sassafe
Takan tashi,
Ta yi addu’o’i
Domin yaranta
Da duk ’yan’uwa:
“Allah, ka kiyaye mu.”
Komin matsalolinta,
Takan rike amincinta,
Tana da kirki.
Koyaushe takan yi wakar nan:
(AMSHI)
‘Zan karfafa ki.
Kar ki ji tsoro.
Ina nan da ke.
Zan kula da ke.’
Yi karfin zuciya.
Tana son wakar nan.
‘Shi zai taimake ki,
Shi zai karfafa ki.’
NA 2
Tana yin sana’a
Don ta iya biyan
Duk bukatun yaranta.
Duk kawayenta
Suna son ta sosai,
Shi ya sa ba ta damu.
3. Tana aiki
Ba hutawa,
Kowane lokaci,
Idan ayyukan
Sun yi mata yawa
Sai ta roki, Ubangiji.
Tana yin kokarinta
Don ta kula da yaranta.
Kuma takan rera
Wakar nan, da ke karfafa ta:
(AMSHI)
‘Zan karfafa ki.
Kar ki ji tsoro.
Ina nan da ke.
Zan kula da ke.’
Yi karfin zuciya.
Tana son wakar nan.
‘Shi zai taimake ki,
Shi zai karfafa ki.’
‘Shi zai taimake ki,
Shi zai karfafa ki.’