Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zan Bauta Maka

Zan Bauta Maka

Ka Saukar

  1. 1. Ya Allah Ubana, ina son in bauta maka.

    Ina son in bauta ma, don in sa ka farin ciki.

    Zan koyar da wadanda ke son su san Kalmarka.

    Don shi ne abin da zai sa in yi farin ciki.

    (KAFIN AMSHI)

    Yin ibada ga Allah shi ne abin da ya fi kyau.

    Zan cika duk alkawurata. Zan bauta maka.

    (AMSHI)

    Ya Uba Jehobah ina yabon ka,

    A shirye nake in bi hanyoyinka.

    Zan bauta maka da dukan karfina.

    Jehobah, ni na ba ka dukan rayuwata.

  2. 2. Yin ibada da kuma kaunar ’yan’uwana

    Su ne abubuwan da na saka gaba farko.

    Na san cewa bayarwa ta fi karba albarka.

    Shi ya sa ina son in taimaka wa mabukata.

    (KAFIN AMSHI)

    Yin ibada ga Allah shi ne abin da ya fi kyau.

    Zan cika duk alkawurana. Zan bauta maka.

    (AMSHI)

    Ya Uba Jehobah ina yabon ka,

    A shirye nake in bi hanyoyinka.

    Zan bauta maka da dukan karfina.

    Jehobah, ni na ba ka dukan rayuwata.

    (AMSHI)

    Ya Uba Jehobah ina yabon ka,

    A shirye nake in bi hanyoyinka.

    Zan bauta maka da dukan karfina.

    Jehobah, ni na ba ka dukan rayuwata.