Zan Maka Godiya
Ka Saukar:
1. Ga fure mai kyau a kan duwatsu
Iska mai dadi, tana busawa sosai,
Rana tana, haskaka ko’ina,
Tsuntsaye kuma, na firewa
(KAFIN AMSHI)
Mene na yi
don wannan gata?
Mene ne zan yi
Don in gode masa?
(AMSHI)
Zan gode ma Allah,
A cikin addu’a
Zan gode ma
Allah don ƙaunarsa.
Zan, dakata,
Na kuma yi tunani sosai, game da
Abubuwan da ya halitta.
Zan gode ma Allah.
Zan gode ma Allah.
2. Abubuwan da ke sararin sama,
Kai ne ka yi su kuma, suna da kyau sosai!
Ga ruwan kogi na gudu ba tsayawa,
Ga taurari ma, na haskakawa—
(KAFIN AMSHI)
Mene na yi
Don wannan gata?
Na san me zan yi
Don in gode masa.
(AMSHI)
Zan gode ma Allah,
A cikin addu’a
Zan gode ma
Allah don ƙaunarsa.
Zan, dakata,
Na kuma yi tunani sosai, game da
Abubuwan da ya halitta.
Zan gode ma Allah.
NA 3
Ina ganin hikimarka
Da duk yawan ƙaunarka,
A halittunka.
Zan gode masa;
Zan gode ma Allah.
(AMSHI)
Zan gode ma Allah,
A cikin addu’a
Zan gode ma
Allah don ƙaunarsa.
Zan, dakata,
Na kuma yi tunani sosai, game da
Abubuwan da ya halitta.
Zan gode ma Allah.
Zan gode ma Allah.
Zan gode ma Allah.