Rumbun Hotuna na Birtaniya na 2 (Satumba 2015 zuwa Agusta 2016)
Shaidun Jehobah da ke kasar Birtaniya suna kaurar da ofishinsu da ke garin Mill Hill a Landan zuwa gabashin birnin Chelmsford, Essex mai nisan kilomita 70. A wannan rumbun hotuna za ka ci gabar da aka samu daga watan Satumba 2015 zuwa Agusta 2016 a aikin da ake yi a sabon ofishinsu.
29 ga Oktoba, 2015—Ainihin wurin da ake aiki
Ma’aikata suna zuba kankare a gaban garejin da za a rika ajiye injunan da za a yi aikin ginin da su.
9 ga Disamba, 2015—Ainihin wurin da ake aiki
Masu aikin gini suna saka rufi a wurin da zai zama ofisoshi da kuma wurin cin abinci ga ma’aikatan a lokacin da ake aikin ginin.
18 ga Janairu, 2016—Ainihin wurin da ake aiki
A hanyar shiga, wani ma’aikaci yana amfani da motar tuge itatuwa don ya tuge wasu itatuwa. Motar tana tuge itatuwan daga jijiyoyinsu zuwa wani wuri. Bayan hakan, masu gyara fili za su dasa itatuwa da yawa a wurin kafin a kammala aikin ginin.
31 ga Maris, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikatan suna cire duk abubuwan da ba sa so da mutanen da suke da wurin a dā suka bari. Kuma hakan zai ba wa kasar sabon fasali don a kara yin gini a wurin.
14 ga Afrilu, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikatan suna amfani da injin daga kaya don su saka bukkoki da za a zauna a ciki na dan lokaci. Ainihin ma’aikatan da kuma wadanda suka zo don su taimaka da aikin za su rika yin amfani da bukkokin a matsayin ofisoshi da kuma wuraren yin hidimomi.
5 ga Mayu, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikatan suna zaɓan abubuwan da za a sake yin amfani da su. Kwamitin da take kaddamar da aikin ginin ta kafa makasudin cewa za a kwashe kashi 95 na abubuwan da ba za su jawo illa daga wurin ba, kuma an cim ma har fiye da hakan ma. Ban da haka ma, an kwashe kashi 89 na shara kamar su tubali da kankare da katakai zuwa wurin da za a sake yin amfani da su a wurin da ake ginin.
23 ga Mayu, 2016—Ainihin wurin da ake aiki
Daya daga cikin ma’aikatan tana binne bututu a kasa. Kuma ta wannan bututun da aka binne ne gidaje da masu aikin ginin suke zama za su rika samun ruwa.
26 ga Mayu, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Wani ma’aikaci yana diban kasar da zai je ya gwada don a san ko za a iya yin amfani da ita a gina hanya a wurin aikin.
31 ga Mayu, 2016—Hoton yadda ofishin zai zama
A ranar 31 ga watan Mayu, 2016, hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ta amince da wannan tsarin ginin. Kuma hukumar kasar ma ta amince da haka, wannan ya ba da damar soma yin aikin ginin.
16 ga Yuni, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikata suna cire abubuwan da ba a bukatar a cikin kasar da aka kwaso daga filin aikin. Kuma abin da suka yi ya ba su damar sake yin amfani da kasar a wani bangare. Wannan aikin ya sa ba za a kashe kudi ba don kwashe kasar daga wurin da za a yi gini ba ko kuma a sayi wani da za a yi amfani da shi ba.
20 ga Yuni, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikata suna gyara wurin da za a yi hanyar shiga. Sun ci gaba da yin aikin duk da cewa wurin ya zama caɓi a watan da ake yawan ruwan sama.
18 ga Yuli, 2016—Ainihin wurin da ake aiki
Ana yayyafa ruwa a hanyar don ya hana kura tashi. Ma’aikatan suna son su kintsa wurin da ake aikin ginin, don yin hakan yana cikin ka’idodin da kungiyar Considerate Constructors ta kafa, wadda kwamitinmu na gine-gine ta yi rajista da ita. Ka’idodin da kungiyar ta kafa wa masu gini ya yi daidai da abin Littafi Mai Tsarki ya ce, wato a rika daraja mutane da kuma nuna wa makwabtanmu mun damu da su.
18 ga Yuli, 2016—Ainihin wurin da ake aiki
Wata tana yanka karfen da zai rike abin da za a daura iyakwandishan a kai.
22 ga Yuli, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikata sun tsame duwatsu daga kasa mai fadin mita 20,000. Kamar yadda aka nuna a hoton ana loda kasa cikin mota. Ana yin amfani da lariya dabam-dabam don a kwashe kasa marar duwatsu. Ana yin amfani da wani inji da yake zuba kasa da aka tankade zuwa manyan motoci.
22 ga Yuli, 2016—Wurin da za a gina ofishin
Ma’aikatan sun yi lebur da kasar sosai don wurin ya yi daidai da zanen ginin da suke bi.
18 ga Agusta, 2016—Wurin da za a gina ofishin
A tsakiyar hoton ta hagu za ka ga wurin da ma’aikatan suka gama yin lebur don a soma gina tushen gidan zama. A can kasa ta hagu, za ka ga gidan da aka kammala don masu aikin ginin su rika zama, kuma ginin zai dauki ma’aikata guda 118.