Rumbun Hotuna na Britaniya na 1 (Janairu zuwa Agusta 2015)
Shaidun Jehobah da ke Britaniya suna kaurar da ofishinsu da ke Mill Hill, Landan zuwa gabashin birnin Chelmsford, Essex mai nisan kilomita 70. A cikin watan Janairu zuwa Agusta 2015, ma’aikata sun soma gyara wurin don a soma aikin gine-gine.
23 ga Janairu, 2015—Wurin da ake gina ofishin
Ma’aikata sun karbi izini daga hukumomi da ke yankin, kuma suka cire itatuwa da suka sare don a iya yin aiki a wurin a nan gaba. Sun yi aiki tukuru don su gama kafin lokacin da tsuntsaye za su soma kafa shekarsu. Suna saka birbishin katakon a hanya don ya yi wa masu tafiya a kasa saukin takawa, kuma an ajiye katakon don a yi amfani da su a gine-ginen.
30 ga Janairu, 2015—Wurin cin abinci
Wani mai gyaran wutan lantarki yana saka soket don ya kafa talabijin a wurin da ake amfani da shi a matsayin otel a dā. Yanzu an mai da wurin zuwa kicin da gidan cin abinci. Talabijin zai sa ma’aikata su rika sauraron ibada ta safiya da kuma Nazarin Hasumiyar Tsaro da ake yi a Bethel.
23 ga Fabrairu—Wurin da ake gina ofishin
Ma’aikata suna saka shinge don su kewaye wurin da ake gine-ginen. Tun da yake wurin kauye ne, sun yi wasu abubuwa don su rage yadda aikin gine-ginen zai shafi dabbobin da ke wurin. Alal misali, sa’ad da suke saka shingen, sun bar fili na kusan santimita 20 don wata dabba mai kama da zomo da ake kira rema su ci gaba da kiwon su.
23 ga Fabrairu—Wurin da ake gina ofishin
Ana gina hanya da za ta hada gidan zama da ainihin wurin da ke gine-ginen.
5 ga Maris, 2015—Wurin da ake gina ofishin
Hoton da aka dauka ta gabas da ke nuna hanyar da aka gina. Kamar yadda yake a can ta dama, hanyar ta kai har wurin da ake ainihin gine-ginen. An mai da gidajen da ke can kasa ta hagu zuwa gidaje da ma’aikatan za su rika kwana. Za a gina gidajen zama a filin da ke kusa da su.
20 ga Afrilu, 2015—Wurin da ake gina gidan zama
Wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da wani wakili daga hedkwatarmu sun ziyarci masu gine-ginen. An yi taro na musamman a wannan makon, kuma an nuna taron a dukan Majami’un Mulkin da ke Britaniya da Ireland. Da yamma kafin a yi taron, an sanar cewa hukumar da ke birnin Chelmsford sun ba da izini a yi gine-ginen.
13 ga Mayu, 2015—Ainihin wurin da ake aiki
Ma’aikata suna kafa wani abu da zai kāre jijiyoyin itatuwa, kuma sun kafa shi tsakanin manyan itatuwa biyu da ake kira oak. Wannan hanyar mahadi ne tsakanin ainihin wurin da ake aikin da kuma wurin da ake gine-ginen, kuma an kafa hanyar ne don kada manyan motoci masu daukan kaya su lalace jijiyoyin itatuwan.
21 ga Mayu, 2015—Wurin gidan zama
Ma’aikata suna haka rami don kafa wasu wayoyi don gidan zama. A hoton an nuna gidaje 50 da masu aikin gine-ginen za su rika kwana a ciki sa’ad da suke aiki.
16 ga Yuni, 2015—Wurin gidan zama
Wani mai aikin famfo yana kafa bututu don wani gidan zama na dan lokaci.
16 ga Yuni, 2015—Wurin gidan zama
Idan ka kalli hoton a ta gabas, an nuna sababbin gidajen zama da aka gina. Kuma a kasa, ana shirya harsashin gini don gina karin gidajen zama. A ta hagu an nuna gidajen da masu aiki a wurin gine-ginen suke kwana, har da gidan abinci. Za a gina ofishin a tsakiyar filin.
16 ga Yuni, 2015—Wurin gidan zama
Wata mai gyarar waya tana hada waya da ke dakin sadarwa. Ana bukatar kwamfuta da Intane sa’ad da aka soma aikin don a gudanar da ayyukan da suka shafi gine-ginen. Kari ga haka, za a rika sadarwa da wasu ofisoshin Shaidun Jehobah kuma hedkwatarmu za su rika taimaka wajen ba da ja-gora.
6 ga Yuli, 2015—Wurin da ake gina ofishin
Wani dan kwangila yana auna ramukan da aka haka ta wurin yin amfani da na’urar GPS. Ramukan suna taimaka wa masu tonan kasa su yi bincike a filin kafin a soma gine-gine. Ko da yake mutanen Roma ne suka zama kusa da birnin Chelmsford, ba a ga kayayyaki na musamman a ramuka 107 da aka haka a lokaci na farko da aka soma bincike a filin ba.
6 ga Yuli, 2015—Ainihin wurin da ake aiki
Ana yanka firam na kofa don ya yi daidai da kofar. Ana gyara wasu gidajen da suke wurin gine-ginen kuma ana mai da su inda za rika yin aiki. A nan ne za a kafa ofisoshi na dan lokaci kuma a rika wasu ayyuka.
6 ga Yuli, 2015—Ainihin wurin da ake aiki
Ana zuba kasa a cikin wata babbar mota don a yi amfani da shi wajen cika inda akwai ramuka.
7 ga Yuli, 2015—Wurin da ake gina ofishin
Hoton da aka dauka daga can nesa da yake nuna ɓangaren ƙasar Britaniya. Da akwai wata hanya mai kyau (ba a nuna hoton ba) da za a iya bi a je bakin teku da tashan jiragen sama da kuma birnin Landan.
23 ga Yuli , 2015—Wurin da ake gina ofishin
’Yan kwangila suna cire gidajen da ke wurin a dā don a soma aikin gina sabon ofishin.
20 ga Agusta , 2015—Ainihin wurin da ake aiki
Wani injin daga kaya yana kafa wani daki. A hoton, an riga an shirya wuraren da za a sāka wasu dakuna. Za a yi amfani da wadannan dakunan a matsayin ofishi da za a rika gudanar da aikin gine-ginen.