Alamar Watchtower—Sananniyar Alama Ce a Brooklyn
Mazauna Birnin New York sun saba ganin alama da ke kan ginin hedkwatar Shaidun Jehobah. Wannan alama ce da aka yi da manyan harufa masu haske kuma tana da tsawon kafa 15 kuma ta yi sama da shekaru 40 yanzu. Babban agogo da ma’aunin yanayi da ke wurin yana taimaka wa yawancin mazauna Birnin su san lokaci da kuma yawan zafi ko sanyin yanayi.
Wata mai suna Eboni tana ganin wannan alamar daga gidanta a Brooklyn kuma ta ce: “Abin farin ciki ne in duba wannan alamar don sanin lokaci da yadda yanayi yake kafin in je aiki. Hakan yana taimaka min in saka tufafi da suka dace da yanayin ranar kuma in je wurin aiki a kan lokaci.”
Wannan alama mai dauke da agogo da ma’aunin yanayi za ta ci gaba da kasancewa a wurin nan da shekara 40 kuma ne? Da kyar. Hakan ya dangana ga wadanda za su sayi ginin da yake ana shirin tare hedkwatar Shaidun Jehobah zuwa arewacin jihar New York.
Akwai wata alama wadda asalin masu ginin suka kafa fiye da shekara 70 da suka shige. Shaidun Jehobah ne suka canza zuwa yadda take a yau bayan da suka sayi ginin a shekara ta 1969.
Alamar tana bukatar a rika kula da ita a kai a kai. Matasa maza dabam-dabam sun yi aiki don kula da wannan alamar, kuma sukan yi gyare-gyaren da ake bukata a kowane lokaci.
Wani mai aiki a wurin da dare ya ce: “IWata rana da yamma wani darektan gidan talabijin ya yi mana waya. Ya kira ne ya gaya mana cewa agogon ya makara da dakikai 15. Ya so mu daidaita agogon don zai yi magana a kai a wani shirin da zai gudanar da daddaren. Ba da dadewa ba sai wani injiniya da yake gyangyadi ya tashi ya soma aiki a kai don ya magance matsalar.”
An sha daidaita wannan agogon don ya kasance daidai kuma ya amfani mutane. Ma’aunin yanayi da ke agogon yana nuni a nau’in Fahrenheit amma a tsakiyar shekara ta 1980, an dada nau’in Celsius a ma’aunin yanayin.
An sauya kwayayen lantarki na neon tubes marasa inganci a shekara ta 2009 da kwayaye masu inganci da ake kira light-emitting diodes kuma hakan ya rage yawan kudin da ake kashewa don gyara, wato fiye da dala 4,000 a shekara. Yanzu wannan alama tana amfani da kashi daya cikin hudu na lantarki da yake amfani da shi a dā.