Koma ka ga abin da ke ciki

An Rage Ofisoshin Rassa na Shaidun Jehobah

An Rage Ofisoshin Rassa na Shaidun Jehobah

A Satumba na shekara ta 2012, an mai da ofisoshin rassa guda 20 na Shaidun Jehobah karkashin ja-gorancin manyan rassa.

Kari ga haka, an bude sababbin rassa a kasashen Sabiya da Makidoniya. Akwai dalilai musamman da suka sa an yi wadannan canje-canjen.

1. Fasaha ta saukaka aikin

A shekarun bayan nan, an sami ci gaba a sadarwa da fasahar buga littattafai kuma hakan ya sa an rage ma’aikata a wasu rassa. Da yake an rage yawan mutane da ke aiki a manyan rassa, an sami gidajen kwana domin wasu da suke aiki a kananan rassa a wasu kasashe.

Yanzu, kowane reshe yana da kwararrun Shaidu da suke kula da aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ofishin reshe na Meziko ne ke kula da aikin wa’azi a kasashen Costa Rica da El Salvador da Guatemala da Honduras da Nicaragua, da kuma Panama. Sakamakon haka, an rufe ofisoshin rassa da ke wadannan kasashe shida.

An tura Shaidun Jehobah guda 40 daga wadannan rassa shida zuwa reshen Meziko don su ci gaba da aikinsu a wurin. Shaidu wajen 95 sun kasance a kasarsu kuma sun soma hidimar wa’azi ta cikakken lokaci.

Wasu kuma a wadannan kasashen Amirka ta tsakiya sun soma aiki a ofisoshin fassara a karkashin ja-gorancin ofishin reshen Meziko. Alal misali, a Panama, wajen Shaidu 20 ne suke fassara Littattafan Shaidun Jehobah zuwa ainihin harsunan mutanen wuraren. Yanzu a ofishin reshe na Guatemala, Shaidu guda 16 ne suke fassara littattafai zuwa harsunan mutanen wurin. Saboda wadannan canje-canjen, an rage ma’aikata a ofishin reshen daga 300 zuwa 75.

2. Ma’aikata za su sami karin lokaci na yin wa’azi

Saboda rage ofisoshin rassa da aka yi, kwararrun masu hidima da suke aiki a kananan rassa za su sa kai ga wa’azin bishara.

Wani mashaidi da aka canja aikinsa zuwa hidimar aikin wa’azi, ya ce: “Daidaita rayuwata da sabon yanayin kalubale ne a ’yan watanni na farko. Amma, yin wa’azi kullum ya sa na kasance da farin ciki kuma na sami albarka sosai. A yanzu haka, ina nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 20, kuma wasu cikinsu suna halartan taro.”