Dubbai Sun Koyi Karatu da Rubutu
A shekara ta 2011, Shaidun Jehobah sun taimaka wa mutane fiye da 5,700 su koyi karatu.
Ghana:
A shekaru 25 da suka shige, mun taimaka wa mutane fiye da 9,000 su koyi karatu da rubutu.
Zambiya:
Tun daga shekara ta 2002, kusan mutane 12,000 sun kara koyan karatu. Agnes, wata ’yar shekara 82 ta ce: “Sa’ad da aka yi sanarwa cewa za a soma wani aji don koya wa mutane da ke ikilisiya karatu, na yi farin cikin yin rajista. A ajin farko, na koyi yadda ake rubuta sunana!”
Peru:
Wata daliba, ’yar shekara 55 ta rubuta cewa: “Ban taba tsammani cewa zan iya karatu da rubutu ba don iyayena ba su sa ni a makaranta ba.”
Mozambique:
Mutane fiye da 19,000 sun koyi karatu a cikin shekaru 15 da suka shige. Wata daliba mai suna Felizarda ta ce: “Ina farin ciki cewa yanzu zan iya karanta Littafi Mai Tsarki ga mutane. A dā yin hakan yana da wuya sosai a gare ni.”
Solomon Islands:
Ofishin reshenmu ya rubuta cewa: “A dā, mutane da yawa da suke zama a wuraren da ke da wuyan zuwa ba su sami damar zuwa makaranta ba. Kari ga haka, yawancin yara ’yan mata ba su yi makarantar boko ba. Saboda haka, mutane da yawa sun amfana daga ajin koyon karatun. Mutane da yawa sun kasance da gaba gadi bayan sun sauke karatu a ajin.”