Taimaka wa ‘Yan Gudun Hijira a Tsakiyar Turai
A shekarun nan, ‘yan gudun hijira da yawa daga Afirka da Gabas ta Tsakiya da kuma Kudancin Asiya sun shiga cikin Turai. Don a taimaka musu, hukumomin jihohi da kuma wadanda suka ba da kansu don su taimaka suna aiki tare don su tallafa musu da abinci da wurin kwana da kuma magani.
Babu shakka, ‘yan gudu hijira suna bukatar taimako sosai. Da yawa a cikinsu suna fargaba don abin da ya faru da su kuma suna bukatar ta’aziya da kuma karfafa. Shaidun Jehobah a tsakiyar Turai suna iya kokarinsu don su tallafa ma wadannan mutanen ta wurin sauraran su da kuma fada musu abin da Littafi Mai Tsarki ya ce don su karfafa su.
Sun Sami Karfafa Daga Littafi Mai Tsarki
Tun daga watan Agusta na 2015, Shaidun Jehobah daga ikilisiyoyi guda 300 a Austria da kuma Jamus sun yi kokarin karfafa wadannan ‘yan gudun hijirar. Sun lura cewa ‘yan gudun hijirar suna son sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da tambayoyi kamar su:
A tsakanin watan Agusta da Oktoba na 2015, Shaidun Jehobah da ke wurin sun yi odar fiye da tan hudu na littattafanmu daga ofishinmu da ke Tsakiyar Turai, kuma sun ba wa ‘yan gudun hijirar wadannan littattafan kyauta.
Yi wa Mutanen Wa’azi a Yarensu
’Yan gudun hijirar da yawa yarensu kadai suke ji. Saboda haka, Shaidun sun yi amfani da dandalinmu na jw.org don su nuna musu littattafai da kuma bidiyoyi da yawa a harsunansu. Matthias da Petra da suka taimaka a birnin Erfurt da ke Jamus sun ce: “A wasu lokuta mukan yi amfani da hotuna ko hannayenmu ko kuma zane don mu yi musu magana.” Kari ga haka, sun yi amfani da JW Language app, wato manhajar koyan harsuna wajen yi wa ‘yan gudun hijirar wa’azi a harsunansu. Wasu kuma sun yi amfani da JW Library da ke harsuna da yawa don su nuna wa ‘yan gudun hijirar bidiyoyi da kuma wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki a harsunansu.
An Sami Sakamako Mai Kyau
Wasu ma’aurata daga birnin Schweinfurt da ke Jamus sun ce, “Mutane da yawa sun zo wurin mu, a cikin sa’o’i biyu da rabi, ‘yan gudun hijirar sun karbi littattafai guda 360 kuma suna ta gode mana.” Wolfgang wanda ya taimaka a birnin Diez da ke Jamus, ya ce: “ ’Yan gudun hijirar sun yi farin ciki cewa muna karfafa su, a wasu lokuta sukan ce mu ba su littattafanmu a harsuna biyar ko shida.”
Da yawa a cikin su sun soma karanta littattafan nan da nan, wasu kuma daga cikinsu sun je don su gode wa Shaidun. Ilonca wani Mashaidin da yake zama a birnin Berlin da ke Jamus ya ce, “Wasu matasa guda biyu sun karbi littattafanmu, bayan minti talatin, sai suka kawo mana kyautar burodi. Kuma suka ba mu hakuri don ba su da wani abin da za su iya ba mu don su nuna godiyarsu.”
“Mun Gode Sosai!”
Masu kula da jama’a da hukumomi da kuma makwabta, sun nuna godiya saboda yadda Shaidun Jehobah suka ba da kansu don su taimaka. Wani da yake kula da ‘yan gudun hijira guda 300 ya ce “Mun gode! Muna godiya sosai da kuka nuna cewa kun damu da mutanen nan!” Har ila wani ya fada wa Shaidun cewa, ba wa ‘yan gudun hijira abin da za su rika karantawa a yarensu yana da kyau sosai, “tun da yake ba wani aiki suke yi yanzu ba.”
Marion da mijinta Stefan da suke zama a kasar Austria, sun bayyana wa ‘yan sanda biyu da suka zo gadin wurin dalilin da ya sa suka ba da kansu don su taimaka. ‘Yan sandan sun gode musu sosai kuma suka karbi littattafai guda biyu. Marion ta ce: “ ’Yan sandan sun yaba mana sosai don aikin da muke yi.”
Wata mata da take zama a Austria kuma tana zuwa sansanin don ba da gudummawar kaya ta lura cewa, ko da yaya yanayin garin yake, Shaidun suna zuwa su tallafa wa ‘yan gudun hijira. Wata rana ta gaya musu cewa: “Babu shakka, ‘yan gudun hijirar suna bukatar taimako, amma abin da suka fi bukata yanzu shi ne karfafa, kuma abin da kuke musu ke nan.”