Wa’azi na Musamman Don A Ceci Rayuka
Domin yawan yadda mutane ke kashe kansu a jihar Tabasco a kasar Meziko, Shaidun Jehobah sun shirya wani wa’azi na musamman na tsawon wata biyu a 2017 don su sake rarraba mujallar Awake! na watan Afrilu 2014 mai jigo “Why Go On?—Three Reasons to Keep Living.” Mutane sun nuna godiya sosai don wannan wa’azi da aka yi.
Taimako a Lokacin da Ake Bukata
Wani Mashaidin Jehobah mai suna Faustino ya tattauna da wata mata da ta damu kwarai game da yanayin yaronta dan shekara 22. Yaron yana fama da bakin ciki har ma ya yi kokarin kashe kansa. Uwar ba ta san yadda za ta taimaka masa ba. Amma da Faustino ya ba ta mujallar, sai ta ce, “Abin da yarona yake bukata ke nan.” Washegari, sai Faustino ya ziyarce yaron, kuma suka tattauna shawarwarin da Littafin Mai Tsarki ya bayar da ke cikin mujallar. Ba da dadewa ba, sai yaron ya soma gyara halinsa. Faustino ya ce, “Yaron ya saki jiki yanzu kuma hankalinsa ya kwanta.” Kari ga haka, yana gaya wa dan’uwansa abubuwan da yake koya, domin dan’uwansa ma yana fama da ciwon bakin ciki.
Wata mai suna Karla da ke zama a birnin Huimanguillo ta yi amfani da mujallar don ta taimaka wa ’yar ajinsu. Karla ta ce: “Na lura cewa wata ʼyar shekara 14 a ajinmu tana cikin bakin ciki kullum. Sai na yi magana da ita kuma ta bayyana mini halin da iyalinta ke ciki. Yayin da muke magana, sai na lura cewa tana da tabo a hannun hagunta.” Ashe yarinyar tana yanka hannunta da kafafunta da gangan. Tana ji cewa ita mummuna ce kuma rayuwarta ba ta da wata ma’ana. Sai Karla ta ba ta mujallar. Bayan yarinyar ta karance mujallar, sai ta gaya wa Karla cewa tana ganin don ita aka rubuta mujallar. Ta yi murmushi kuma ta ce yanzu ta gane cewa rayuwa tana da ma’ana.
Wani mutum a birnin Villahermosa ya damu kwarai. An sallame shi daga aiki kuma matarsa ta gudu ta bar shi da yara. Ya roki Allah ya taimake shi amma bai ga mafita ba. Yana gab da kashe kansa ke nan, sai wasu Shaidun Jehobah biyu, wato Martín da Migue suka kwankwasa kofarsa. Da mutumin ya bude kofar, sai Shaidun suka mika masa mujallar. Da mutumin ya ga jigon, sai ya ji kamar Allah ne ya amsa addu’arsa. Martín da Miguel sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su karfafa shi. Bayan ’yan kwanaki sai suka sake ziyartar sa kuma suka tarar da shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Yanzu suna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutumin sau biyu a mako.
An Yi wa Fursunoni Wa’azi
An yi wa mutanen da ke tsare a gidan yari ma wa’azi. Shaidun Jehobah sun ziyarci gidajen yari da yawa a jihar Tabasco don su nuna masu shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka masu su ji dadin rayuwa. Shaidun sun shirya bidiyoyi da jawabi kuma sun tattauna dalilan ci gaba da rayuwa da aka wallafa a mujallar. Fursunoni da ma’aikantan gidan yarin sun ji dadin ziyarar. Alal misali, wani fursuna ya ce: “Na yi kokarin kashe kaina sau uku. Wasu mutane sun ce mini Allah yana kauna ta, amma ba su taba amfani da Littafi Mai Tsarki don su tabbatar mini da hakan ba. Kalmominku sun karfafa ni kwarai da gaske.”
Mutane da yawa sun ga amfanin wannan wa’azi na musamman. Sakataren kiwon lafiya na jihar ya yi wa Shaidun Jehobah godiya domin kokarin da suka yi don su taimaka wa jama’a. An wallafa wani talifi a wata jarida mai jigo “Sun Fita Don Su Yaki Kisan Kai” kuma talifin game da wannan wa’azi da aka yi ne.