Yadda Ake Yi wa Matukan Jirgin Ruwa Wa’azi
Binciken da aka yi ya nuna cewa akwai kimanin mutane miliyan daya da rabi a fadin duniya da suke tuka jirgin ruwa. Da yake masu tuka jirgin ruwa suna zuwa tashoshin jiragen ruwa dabam-dabam, ta yaya Shaidun Jehobah za su iya yi musu wa’azi? A duk lokacin da jiragen ruwa suka zo tasharsu, Shaidun Jehobah da aka horar suna neman izini don su shiga jirgin su yi jawabi kuma su ba wa ma’aikatan littattafai kyauta a yaren da suke so.
Mene ne aka cim ma ta yin hakan? Wani Mashaidi mai suna Stefano da ya ba da kai don ya rika zuwa tashar jirgin ruwa da ke birnin Vancouver a kasar Kanada yin wa’azi ya ce: “Wasu mutane suna tunanin cewa duka masu tuka jirgin ruwa mutane ne da ba su da kan gado kuma ba sa mu’amala da wasu. Watakila wasun su haka suke, amma wadanda muka hadu da su mutane ne masu saukin kai kuma suna son mu koya musu Littafi Mai Tsarki.” Stefano ya kara cewa: “Yawancinsu sun yi imani da Allah kuma suna son samun albarka, don haka, suna sauraron mu idan muka zo musu wa’azi.” A tsakanin Satumba na 2015 da kuma Agusta na 2016 a birnin Vancouver kadai, an gayyaci Shaidun Jehobah fiye da sau 1,600 don su shigo jirgi su yi wa’azi! Kuma ma’aikata a jiragen ruwa sun karbi dubban littattafai a yaruka dabam-dabam, kuma fiye da 1,100 a cikinsu sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki.
Ta yaya aka ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da masu tuka jirgin ruwa?
Da yake Shaidun Jehobah a fadin duniya suna zuwa tashoshin jiragen ruwa yin wa’azi, matukan jiragen da suke son su ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki suna iya tuntubar Shaidun Jehobah a duk tashar jirgin ruwa da suka je. Alal misali, a watan Mayu na 2016, Shaidun Jehobah a birnin Vancouver sun hadu da Warlito shugaban masu dafa abinci a jirgin ruwa. Kuma suka nuna masa bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? Bayan haka, suka soma nazari da littafin nan Albishiri Daga Allah! Warlito ya ji dadin nazarin da ake yi da shi kuma yana so ya ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, amma wurin da jirgin ruwansu zai tsaya shi ne a tashar da ke birnin Paranaguá a kasar Brazil.
Sa’ad da jirginsu ya iso tashar jirgin ruwa da ke birnin Paranaguá bayan kusan wata daya, Warlito ya yi mamaki sosai da ya ga Shaidun Jehobah suka zo tashar suna neman shi kuma suka kira shi da suna. Sun fada masa cewa ‘yan’uwansu a birnin Vancouver sun turo musu sako cewa yana neman wadanda za su yi nazari da shi. Warlito ya yi farin ciki sosai da ya hadu da wadannan Shaidun Jehobah na kasar Brazil kuma ya nuna godiyarsa don yadda aka tsara a taimaka masa. Ban da haka ma, ya ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah a duk tashar jirgin ruwa da suka je.