Koma ka ga abin da ke ciki

Hasumiyar Tsaro a Turanci Mai Sauƙi

Hasumiyar Tsaro a Turanci Mai Sauƙi

Somawa da fitar Yuli na 2011, an fitar da Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi a gwada a gani na shekara guda. Yanzu an gama gwajin, sakamakon shi ne za a ci gaba da buga ta.

Somawa da Janairu na 2013, za a soma buga harsunan French, Portuguese, da na Spanish masu sauƙi.

An shirya wannan bugu mai sauƙi domin ya taimaka wa waɗanda suke halartan taron ikilisiya na Turanci a Majami’ar Mulki amma ba ga waɗanda Turanci ba yarensu ba ne.

Tun fitarta na farko mutane sun rubuto wasiƙun godiya da yawa. Mai suna Rebecca mai shekara 64 da take zama a Liberiya da ba ta yi makaranta ba sam ce ta rubuta wata wasiƙar. Ta ce: “Ina koyon karatu. A wasu lokuta nakan karanta Hasumiyar Tsaro a Turanci amma ba na fahimtawa. Na so bugun mai sauƙin nan sosai. Na fi fahimtarta.”

Iyaye da yawa suna amfani da bugu mai sauƙin don su taimaka wa yaransu su shirya Nazarin Hasumiyar Tsaro, ɗaya cikin taro na Shaidun Jehobah.

Rosemary, wadda take renon jikoki uku mata, ta ce: “Yin nazarin Hasumiyar Tsaro tare da yaran ya zama mini matsala. Dole mu ɗauki ƙamus muna bincika kalmomi da yawa. Sai mu ci lokaci mai yawa a ƙoƙarin fahimtar kalmomin cikin talifin da yake sa yaran sau da yawa ba sa fahimta shi. Yanzu muna amfani da lokaci akan nassosi kuma mu binciki yadda suka shafi darasin.”

Ga misalin yadda ainihin turancin ya bambanta daga mai sauƙin. A yadda ya kwatanta taron mazannin Kristi a Ayyukan Manzanni sura ta 15, ainihin Turanci ya ce: “What followed was, not a mind-numbing theological debate over dry technicalities, but a lively doctrinal discussion.” Ga Turanci mai sauƙin: “Their meeting was, not a boring religious argument about unimportant details, but an exciting discussion about Bible teachings.”