Koma ka ga abin da ke ciki

Hotunan da Ke Kara Kyaun Littattafanmu

Hotunan da Ke Kara Kyaun Littattafanmu

Ta yaya masu daukan hotunanmu suke daukan hoton da ke kara kyaun littattafanmu kuma su fitar da ma’anarsa? Bari mu yi la’akari da yadda aka dauki hoton bangon mujallar Awake na watan Satumba 2015 don mu bayyana yadda ake yin hakan. *

  • Zane-Zane. Bayan an karanta talifin nan “A Balanced View of Money,” masu zane-zane da ke Sashen Yin Zane a Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, New York, a Amirka sun zana hotunan da za su bayyana yadda ake so mujallar ta zama. Bayan haka, sai suka nuna wa Kwamitin Rubuce-Rubuce na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah don su duba kuma su zabi wanda za a yi amfani da shi.

    Wasu hotunan bangon mujallar da Kwamitin Rubuce-Rubuce suka duba

  • Wuri. Maimakon a je banki don a dauki hoton, masu daukan hotonmu sun tsara wani zauren da ke Cibiyar Koyarwa ta Watchtower kuma suka mai da wurin ya zama kamar banki. *

  • ’Yan wasa. Dukan ’yan wasan Shaidun Jehobah ne kuma an yi amfani da su a matsayin abokan cinikayya daga wurare dabam-dabam da suka zo banki. Bayan an dauki hoton sai a adana don kada a rika yawan amfani da hotunan ’yan wasa iri daya.

  • Kayan da aka yi amfani da su. Sashen Yin Zane sun yi amfani da kudin wata kasa don a nuna cewa bankin ba a kasar Amirka take ba. Masu daukan hoton sun yi amfani da abubuwa da dama don hoton ya kasance kamar a banki aka dauka. Wani mai daukan hoton mai suna Craig ya ce: “Muna mai da hankali sosai don mu yi aikin da kyau.”

  • Sutura da kayan kwalliya. ’Yan wasan ne suka kawo kayansu a hoton da aka dauka a bankin. Amma Sashen Yin Zane ne suke yin bincike kuma su yi kayan da za a yi amfani da su idan ana so a dauki hoto game da tarihi ko kuma idan akwai kaya na musamman da ake so a yi amfani da su. Masu kwalliya ne suke yi wa ’yan wasan kwalliyar da ta dace da abin da ake so a fitar a hoton. Craig ya ce: “A yau, ana dauka hotuna masu kyau sosai. Don haka, muna bukatar mu mai da hankali don kada wani abu ya lalata hoton.”

  • Daukan Hoto. Masu daukan hoton sun tabbatar da cewa hasken da ke bankin ya nuna cewa an dauki hoton ne a lokacin da mutane suke zuwa banki. Masu dukan hoto suna bukatar su tabbatar da cewa hasken ya dace da lokacin da aka dauki hoton. Craig ya ce: “Tun da ba bidiyo ba ne, muna bukatar haske sosai domin wannan hoton ne zai nuna abin da ake so a bayyana.”

  • Tace hoto. Bayan an gama daukan hoton, masu tace hoto sun tace hoton a hanyar da ba za a iya gane irin kudin da aka yin amfani da shi ba. Sun yi hakan don masu karatu su mai da hankali ga mutanen da suke cikin hoton ba kudin ba. Ko da yake kalar tagar da kuma firam din bankin ja ne, masu tace hoton sun canja kalar zuwa kore don kalar ta yi daidai da wanda yake cikin hoto.

Ban da hotunan da ake daukawa a Patterson, ofishin Shaidun Jehobah a dukan fadin duniya kamar wadanda suke Ostareliya da Brazil da Kanada da Jamus da Japan da Malawi da Koriya da kuma Afirka ta Kudu suna da masu daukan hoton da za su iya daukan hotunan da za a yi amfani da su a littattafanmu. A kowace wata, Sashen Yin Zane da ke Patterson suna saka hotuna guda 2,500 a inda ake adana su. Ana amfani da yawancinsu a mujallunmu na Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! Kuma a shekara ta 2015, an rarraba kofi miliyan 115 na wannan mujallun. Muna gayyatar ku ku zo yawon bude ido a ofishinmu da ke Patterson, a Amirka ko kuma wani ofishi dabam don ku samu karin bayani.

Ba da mujallar a wa’azi

^ sakin layi na 2 An dauki hotuna da yawa don bangon mujallun. Amma ba a yi amfani da dukansu ba. Maimakon haka, ana adana hotunan don a iya yin amfani da su a wani aiki dabam.

^ sakin layi na 4 Idan ana so a dauki hoto a kan hanya, Sashen Yin Zane suna bukatar su karbi izini daga hukumomin kuma za su fadi yawan mutanen, da kayan aiki da kuma irin hasken da za su yi amfani da su.