Littattafan da Aka Fassara Zuwa Yaren Kurame Na Quebec Yana Biyan Bukata
A gabashin Kanada inda ake yaren Faransanci, yawancin kurame suna amfani da fassarar harshen Quebec (LSQ). * Domin Kurame 6,000 ne kawai ke al’ummar, saboda haka babu isashen littattafai a harshen kurame na Quebec. Hakazalika, domin a taimaka wa mutane su gane Littafi Mai Tsarki, Shaidun Jehobah sun kara kokari domin su buga littattafai a harshen kurame na Quebec a kyauta.
Domin a gane muhimmancin kokarin da aka yi a wannan aikin fassara, bari mu yi la’akari da labarin Marcel. An haife shi a shekara ta 1941 a lardin Quebec na kasar Kanada. Shekara biyu da haihuwarsa sai ya kamu da ciwon sankarau, a sakamakon haka ne ya zama kurma. Mercel ya ce “Da na cika shekara tara, sai na fara halartar makarantar kurame, a can na koyi harshen yaren kurame na Quebec. Ko da yake akwai takardu da ke koyar da kalilan sani a yaren kurame, babu littattafai a yaren kurame.”
Me ya sa yake da muhimmanci a wallafa littattafai a harshen yaren kurame na Quebec? Mercel ya ba da amsar: “Kurame suna bukatar su karanta abu a cikin yaren da za su sami cikakkiyar ganewa ba tare da wata matsala ba. Idan babu littattafai a harshen yaren kurame na Quebec, dole ne mu dogara ga kalaman baki—kuma ba za mu fahimci abubuwa da yawa ba!”
Domin a biya bukatar Marcel da wasu kuramen da ke amfani da harshen yaren kurame na Quebec, Shaidun Jehobah sun fitar da littafinsu na farko a harshen yaren kurame a 2005. A kwanan nan, sun fadada ofishinsu na fassara a birnin Montreal, Quebec. A yanzu ma’aikata a ofishin sun kai bakwai wadanda ke aiki na cikakken lokaci kuma sama da dozin daya wadanda suke aiki na dan lokaci. An shirya su a kungiyoyi uku, kuma suna amfani da studio guda biyu da ke da ingantacciyar kayayyakin aiki domin shirya bidiyoyi a harshen yaren kurame na Quebec.
Mutanen da ke amfani da harshen yaren kurame na Quebec sun yaba wa ingantacciyar littattafan da Shaidun Jehobah suka wallafa. Stephan Jacques, wanda yake mataimakin darekta na Association des Sourds de l’Estrue, * ya ce: “An shirya littattafansu yadda ya kamata. Alamun na da saukin ganewa, kuma bayanin da ke fuskokin hotunan na da kyau. Na yaba wa wadanda ke cikin bidiyon a yadda suka suturtar da kansu.”
Hasumiyar Tsaro, mujallar da ake amfani da ita a kowace mako a taron Shaidun Jehobah a fadin duniya, a yanzu dai ana samunsa a harshen yaren kurame na Quebec domin Shaidun Jehobah 220 tare da wadanda ke halartar taruwai a ikilisiyoyin harshen yaren kurame bakwai da rukunai a Quebec. Bugu da kari, Shaidun Jehobah sun ci gaba da shirya bidiyoyi cikin harshen yaren kurame a intane, wanda ya kunshi wakoki masu motsawa daga Littafi Mai Tsarki.
Marcel, wanda aka ambata daga farko, na murnar samo littattafai a harshen yaren kurame na Quebec. * Wadanda Shaidun Jehobah suka wallafa ne ya fi burge shi. “Abin farin ciki ne ganin bidiyoyi da yawa na harshen yaren kurame na Quebec a dandalin jw.org.” Ya ce: “Ina jin dadin koyarwar a yare na da na fi ganewa.”
^ sakin layi na 2 Fassarar yaren kurame na LSQ (a yadda yake a faransanci Langue des signes québécoise) yaren kurame ne na musamman, ko da yake yana nan kusa da tsarin yaren kurame na Amirka.
^ sakin layi na 6 Kungiyar agaza wa kurame a Quebec.
^ sakin layi na 8 An fara buga Hasumiyar Tsaro ta nazari na kowane wata a cikin harshen yaren kurame na Quebec daga Janairu 2017.