Karatun Littafi Mai Tsarki da Mutane Fiye da Dari Suka Yi
“Yana jan hankalin mutane sosai kuma ya sa su tunani.”
“Yana sa ka ga kamar abubuwan da kake karantawa a cikin Littafi Mai Tsarki suna faruwa yanzu.”
“Yana da jan hankali sosai kuma ya sa ni ji kamar yanzu ne abubuwan da na dade ina karantawa suke faruwa.”
Furucin da wadanda suka saurari karatun littafin Matta a dandalin jw.org na Turanci suka yi ke nan.
A shekara ta 1978 ne Shaidun Jehobah suka fara fitar da karatun Littafi Mai Tsarki a faifai. Daga baya, an fitar da rabi ko kuma cikakken karatun wancan juyin Littafi Mai Tsarki a harsuna 20.
Amma yanzu ana bukatar a fitar da wani sabon karatun Littafi Mai Tsarki domin sabon fassarar New World Translation da aka fitar a shekara ta 2013. Amma akasin wancan tsohon karatun da mutane uku ne suka yi, a wannan sabon karatun an yi amfani da muryoyi dabam-dabam don mutane fiye da 1000 da aka ambata a Littafi Mai Tsarki.
Yin amfani da muryoyi dabam-dabam zai taimaka wa masu sauraro su ga kamar labarin da suke saurara yana faruwa yanzu. Karatun ba daya yake da karatun Littafi Mai Tsarki da ake saurara ba domin ba shi da kida da kuma sauti na musamman, amma duk da haka yana sa mutum ya ji kamar abubuwan da yake saurara suna faruwa yanzu.
Irin wannan babban aiki da ke bukatar masu karatu da yawa yana bukatar shiri sosai. Da farko, masu bincike sun yi kokari su gano wanda ke magana a kowane nassi da ma’anar nassin da kuma yadda wadanda aka ambata a cikin labarin suke ji. Alal misali, idan aka yi kaulin wani manzo amma ba a ambaci sunansa a cikin labarin ba, muryar wane ne ya kamata a yi amfani da shi? Idan aka ga wani furuci da ke nuna rashin yarda, ana iya cewa Toma ne ya yi maganar, amma idan aka ga wanda ke nuna mutum mai garaje, ana iya cewa Bitrus ne ya yi maganar.
An kuma tabbata cewa shekarun masu karatun ya yi daidai da na wadanda aka ambata a cikin labarin. Alal misali, an yi amfani da muryar matashi a labarin manzo Yohanna sa’ad da yake matashi, sa’an nan an yi amfani da muryar tsoho a labarin manzo Yohanna a lokacin da ya tsufa.
Kari ga haka, an nemi wadanda suka iya karatu sosai. Yawancin wadanda aka yi amfani da su masu hidima ne a ofishin Shaidun Jehobah a Amirka. An gwada wadanda aka zaba don a tabbata ko za su iya karatun da kyau kuma aka ce su shirya don su karanta wani sakin layi a cikin mujallar Awake!. Kari ga haka, an sa su karanta labarai a cikin Littafi Mai Tsarki da ke nuna fushi ko bakin ciki ko murna ko kuma sanyin gwiwa. Ta wurin wannan gwajin ne aka tabbatar da wadanda za su iya yin karatu da kyau kuma aka san irin karatun da ya fi dacewa da su.
Da zarar an ba mutum sashen da zai karanta, yana zuwa daya daga cikin dakunan daukan murya da muke da su a ofishinmu na Brooklyn ko Patterson ko kuma Wallkill don a dauki karatun. Kwach da ke ja-gorar karatun yana tabbata cewa mai karatun ya yi amfani da muryar da ta dace. Ana ba kwach da mai karatun takarda na musamman da ke ba da ja-gora a kan inda ya kamata a dakata a karatun da kuma yadda za a kara ko kuma a rage murya. Kari ga haka, kowane kwach yana amfani da karatun tsohon juyin New World Translation don ja-gora.
Ana yin wasu gyare-gyare a cikin dakin daukan murya yayin da ake daukan muryoyin. Akan harhada kalmomi ko sakin layi da aka dauka sau da sau domin a sami karatun da ya fi kyau.
Ba a san yawan lokaci da za a yi ana daukan karatun wannan juyin New World Translation na 2013 gaba daya ba. Amma a duk lokacin da aka gama daukan karatun wani littafi a cikin Littafi Mai Tsarki, za a saka karatun a dandalinmu na jw.org a karkashin “Books of the Bible” kuma za a saka alama kusa da sunan littafin da zai nuna cewa za a iya sauraron karatun littafin.