Amon Waka a Harsuna da Yawa
Idan fassara waka daya zuwa wani yare ba karamin aiki ba ne, fassara littafin waka mai wakoki 135 gaba daya fa? Babu shakka, jan aiki ne sosai!
Shaidun Jehobah sun fuskanci wannan kalubalen kuma a shekara uku sun fassara littafin waka gaba daya, wato Sing to Jehovah, zuwa harsuna 116. An fassara wata karamar nau’i littafin waka mai wakoki 55 cikin karin harsuna 55. Wasu harsuna da dama suna kan fassarawa.
Rubuta Waka da Kuma Fassarawa
Shaidun Jehobah suna fassara littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki cikin harsuna wajen 600, kuma ana samun littattafai cikin harsuna wajen 400 na wadannan harsunan a dandalinmu na Yanar gizo. Amma fassara littafin waka yana tattare da kalubale na musamman. Me ya sa? Domin ba a canja karin wakoki na Sing to Jehovah ba duk da cewa an fassara wakokin zuwa harsuna da yawa.
Tsara kalmomi zuwa waka ya bambanta sosai da fassara kalmomi zuwa wani yare. Alal misali sa’ad da masu fassara suke fassara mujallar Hasumiyar Tsaro, sukan fassara dukan ma’anar daga yaren da suke fassarawa. Amma shirya waka ba haka ba ne.
Tsarin da Ake Bi
Sa’ad da mafassara suke fassara waka, sukan bi tsarin da ya dan bambanta da wanda suke bi sa’ad da suke fassara wasu bayanai dabam, domin wajabi ne kalmomin waka su kasance da ma’ana da fasaha kuma da saukin tunawa.
Ya kamata kalmomin da aka yi amfani da su a wakar yabo su kasance masu sauki sosai don mai waka ya fahimci ma’ana da manufarsu nan take. A kowane yare, ana bukatar kalmomin su jitu da amon don wakar ta zama da dadin ji kuma ta kasance kamar a yaren ne ainihin mawakin ya yi wakar.
Ta yaya mafassara suke cim ma wannan burin? Maimakon fassara kalmomin kai tsaye daga kalmomin Turanci na Sing to Jehovah, an shawarci rukunin mafassara su rubuta sabbabin kalmomin waka masu sosa rai yadda ainihin wakar take sosa rai. Ko da yake mafassara sukan yi kokarin bin ma’anar nassin da wakar ke bayyanawa, sukan yi amfani da kalmomin da ake amfani da su yau da kullum a yarensu, wadanda suke da sauki a tuna da su.
Mataki na farko shi ne fassara wakar daga wakar Turanci kai tsaye. Bayan haka, mashaidi da ya kware a rubuta waka zai sarrafa wadannan kamomin da aka fassara don su kasance da fasaha da ma’ana a sabon yaren. Da yake ana mai da hankali ga ainihin ma’anar nassi, bayan mai rubuta wakar ya gama aikinsa, sai mafassara su sake bincika wannan da aka fassara don su tabbata cewa komi ya yi daidai.
Shaidun Jehobah a dukan duniya sun yi murna sosai da suka sami sabon littafin waka, kuma ana zaton samun littafi a cikin harsuna da yawa.