Shafuffuka Kadan, Harsuna da Yawa
Somawa daga Janairu 2013, za a rage yawan shafuffukan Mujallun Awake! da kuma Hasumiyar Tsaro na wa’azi daga 32 zuwa 16 a kowace fitowa.
Yanzu bayanai da za su riƙa kasancewa a waɗannan mujallun za su ragu kuma hakan zai sa a fassara mujallun a harsuna da yawa fiye da dā. Alal misali, an wallafa mujallar Awake! ta Disamba 2012 cikin harsuna 84, da kuma Hasumiyar Tsaro ta Disamba 2012 a cikin harsuna 195. Amma, a Janairu 2013, ana wallafa mujallar Awake! a cikin harsuna 98 kuma Hasumiya Tsaro a cikin harsuna 204.
Za a ci gaba da wallafa mujallar Hasumiya Tsaro na nazari cikin shafuffuka 32.
Shafuffuka Na Zahiri Kadan—Shafuffuka Na Intane da Yawa
Waɗannan canje-canjen da za a yi ga mujallunmu da ake bugawa zai shafi www.pr418.com, wato dandalinmu na Yanar Gizo a hanyoyi biyu.
Wasu abubuwan da ake wallafawa a mujallunmu za su riƙa fita a wannan dandalin ne kawai. Alal misali, talifofi irin su “Don Matasa,” “Abin da Na Koya Daga Littafi Mai Tsarki,” rahoton saukar daliban Gilead wadanda ake bugawa a Hasumiyar Tsaro na wa’azi dā, da kuma talifofin nan “Don Nazari na Iyali” “Tambayoyin Matasa” da suke fita a Mujallar Awake! yanzu za su riƙa fita a Intane ne kawai.
Za a riƙa samun mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! a wata karin nau’i na kwamfuta. An yi shekaru da dama ana saka nau’in PDF din mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! a dandalin www.pr418.com. Yanzu za a riƙa samun waɗannan mujallun a nau’in HTML. Nau’in nan zai sa a iya a bude mujallun da sauki kuma a karanta su kai tsaye daga kwamfutar cikin gida ko kuma karamar na’ura. Kari ga haka, za ka iya samun wasu littattafan da aka wallafa cikin harsuna 400 a dandalin.