Kuna Guje wa Mutanen da Suka Bar Addininku?
Shaidun Jehobah da suka yi baftisma amma suka daina yin wa’azi kuma wataƙila ma sun daina yin hulɗa tare da masu bi, ba ma guje musu. Maimakon haka, mu kan yi ƙoƙarin mu taimaka musu su sake fara dangantaka da Jehobah.
Ba ma kawai yanke zumunci da mutumin da ya yi zunubi. Amma, idan Mashaidi da ya yi baftisma ya ci gaba da taka dokar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma bai tuba ba, za a guje shi ko kuma a yi masa yakan zumunci. Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa: “Ku fitarda mugun nan daga cikinku.”—1 Korinthiyawa 5:13.
Me za a ce game da mutumin da aka yi wa yankan zumunci amma matarsa da yaransa Shaidun Jehobah ne? Hakan zai shafi dangantakarsu ta addini, amma ba za ta shafi dangantakarsu ta jiki ba. Za su ci gaba da zaman aure da ƙauna ta iyali.
Waɗanda aka yanke zumunci da su za su iya halartar taronmu na addini. Idan sun yarda, dattawan ikilisiya za su iya taimaka musu a ruhaniya. Dalilin yin haka shine a taimaka musu su sake cancantar zama Shaidun Jehobah. Ana marabtar duk waɗanda aka yanke zumunci da su a ikilisiya da suka daina halaye marasa kyau kuma suka nuna tabbacin suna rayuwa bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.