Me Ya Sa Ba Ku Yarda da Karin Jini?
Kurakure da Ake Yawan Yi
Kage: Shaidun Jehobah ba su gaskata da cewa likitoci za su iya taimaka musu a lokacin da suke ciwo ba, domin haka ba sa bukatar taimakonsu.
Gaskiya: Muna yi wa kanmu da iyalanmu jinyar da ta dace. Idan ba mu da lafiya, muna zuwa wurin likitocin da suka kware don su ba mu magani ko kuma su yi mana fida ba tare da karin jini ba. Muna jin dadin ci gaba da aka samu ta hanyar kimiyyar magani. Hakika, mutane yanzu suna amfani da hanyar yin magani ba tare da jini ba da a dā ake yi wa Shaidu ne kadai. A kasashe da yawa yanzu, duk wani mai rashin lafiya yana da izinin ya ki da wani magani ko wata jinyar da za a yi ta wurin karin jini, saboda cutar da ke cikin jini, da wadanda za su raunana jiki har da kurakuren da likitoci ke yi.
Kage: Shaidun Jehobah sun gaskata cewa bangaskiyar mutum zai warkar da cutar da yake da shi.
Gaskiya: Ba mu gaskata cewa bangaskiyar mutum zai warkar da cutarsa ba.
Kage: Ki da karin jini ya fi muni.
Gaskiya: Yin jinya ba tare da jini ba ya fi amfani. a
Kage: Shaidun Jehobah da yawa har da yara suna mutuwa kowace shekara domin sun ki da karin jini.
Gaskiya: Wannan ba gaskiya ba ne sam. Likitoci masu fida sau da yawa suna yin fida mai wuya irin su fidar zuciya da kashi da kuma saka wa mutum wata gabar jiki. b Masu rashin lafiya, manya da yara da ba a yi musu karin jini ba suna samun sauki da koshin lafiya fiye da wadanda aka yi musu karin jini. c Hakika, babu wanda zai iya ba da tabbaci cewa mutum zai mutu idan ba a yi masa karin jini ba ko kuma cewa zai rayu idan aka yi masa karin jini.
Me ya sa Shaidun Jehobah ba sa yarda a yi musu karin jini?
Wannan ba batun maganin jinya ba ne kadai amma na addini ne. Sabon alkawari da kuma tsohon alkawari sun ce mu hanu daga jini. (Farawa 9:4; Levitikus 17:10; Kubawar Shari’a 12:23; Ayyukan Manzanni 15:28, 29) Kari ga haka, Allah yana daukan jini a matsayin rai. (Levitikus 17:14) Saboda haka, muna ki da karin jini ba kawai don mu yi wa Allah biyayya ba, amma kuma don mun girmama shi a matsayin Wanda ya ba mu rai.
An yi canji da yawa a ra’ayi
A dā, masu kimiyyar magani suna daukan hanyoyin yin fida ba tare da karin jini ba cewa matakin kisan kai ne, amma yanzu sun canza wannan ra’ayin. Alal misali, a shekara ta 2004, wani talifi da aka wallafa cikin wata mujallar ilimin kimiyyar magani ta ce “a nan gaba za a soma yin amfani da hanyoyi da yawa da Shaidun Jehobah suke amfani da su wajen jinya.” d A shekara ta 2010, wani talifi da ke cikin mujallar nan Heart, Lung and Circulation ya ce “ba Shaidun Jehobah kadai ba ne za a rika ‘yi musu fida ba tare da yin karin jini’ ba, amma ya kamata masu fida su soma amfani da wadannan hanyoyin a ayyukansu na kullum.”
Dubban likitoci a dukan duniya suna amfani da hanyoyin yin fida ba tare da karin jini ba. Kasashe da suke tasowa ma suna amfani da irin wadannan hanyar yin magani da ba a bukatar karin jini, mutane da yawa ma da ba Shaidun Jehobah ba suna neman a yi musu irin wannan jinyar.
a Ka duba littafin nan Transfusion and Apheresis Science, kundi na 33, lamba 3, shafi na 349.
b Ka duba The Journal of Thoracic and Cardiovascular Surgery, Kundi na 134, Lamba 2, shafuffuka na 287-288; da Texas Heart Institute Journal, Kundi na 38, Lamba 5, shafi na 563; Basics of Blood Management, shafi na 2; da Continuing Education in Anaesthesia, Critical Care & Pain, Kundi na 4, Lamba 2, shafi na 39.
c Ka duba The Journal of Thoracic and Cardiovascular Surgery, Kundi na 89, Lamba 6, shafi na 918; da Heart, Lung and Circulation, Kundi na 19, shafi na 658.
d Continuing Education in Anaesthesia, Critical Care & Pain, Kundi na 4, Lamba 2, shafi na 39.