Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suke Zuwan Wajen Waɗanda Suke da Nasu Addini?
Mun fahimci cewa mutane da yawa da suke da addininsu suna jin daɗin tattauna batutuwan Littafi Mai Tsarki. Hakika, muna daraja ra’ayin imanin da mutum yake da shi da ke dabam da namu, kuma ba ma tilasta wa mutane su ji saƙonmu.
Yayin da muke tattaunawa game da addini, mu kan yi ƙoƙarin yin haka bisa shawarar da ke Littafi Mai Tsarki mu yi hakan da “ladabi” da “tsoro.” (1 Bitrus 3:15) Mun san cewa wasu za su ƙi saƙon da muke tafe da shi. (Matta 10:14) Amma, ba za mu san yadda mutane za su amsa ba sai bayan mun yi magana da su. Mun kuma fahimci cewa yanayin mutane yakan canza. Alal misali, a wani sa’i mutum ba zai sami zarafin yin magana da mu ba amma kuma a wani sa’in sai ya so yin zance da mu. Kuma mutane sukan fuskanci sababbin matsaloli ko kuma yanayi, hakan zai sa su yi marmarin saƙon Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, muna ƙoƙarin yin magana da mutane a dukan yanayi.