Mene ne Ra’ayin Shaidun Jehobah game da Kimiyya?
Muna daraja abubuwan da ’yan kimiyya suka kirkiro, ban da haka ma, muna gaskatawa da duk wani ra’ayinsu da ya jitu da tabbacin da muke gani.
Wani kamus ya bayyana ma’anar kimiyya cewa: Nazarin halittu ne da yadda suke yin abubuwa da kuma amfani da muke samuwa daga wurin su. Ko da yake Littafi Mai Tsarki ba littafin kimiyya ba ne, ya karfafa mutane su bincika halittu kuma su amfana daga wasu abubuwan da ’yan kimiyya suka binciko. Ka yi la’akari da wasu misalai:
Ilimin Taurari: “Ku ta da idanunku sama, ku duba ko wane ne ya halicci wadannan, wanda ya kawo rundunansu bisa ga lissafinsu: yana kiransu duka da sunansu.”—Ishaya 40:26.
Ilimin Halittu: Sulemanu “ya yi zancen itatuwa, tun daga cedar da ke cikin Lebanon har zuwa hyssop wanda ke tsirowa daga cikin bango: ya kuma yi zancen bisashe da tsuntsaye da masu-rarrafe da kifaye.”—1 Sarakuna 4:33.
Magani: “Masu-lafiya ba su da bukatar mai-magani; sai dai masu-cuta.”—Luka 5:31.
Ilimin Yanayi: “Ka taba shiga rumbunan snow (dusan kankara), ka taba ganin rumbunan kankara . . . Yaya ake watsa iskan gabas a kan duniya?”—Ayuba 38:22-24.
Littattafanmu suna daraja kimiyya shi ya sa suke wallafa talifofin da suka yi magana game da halittu da kuma abubuwan da ‘yan kimiyya suka cim ma. Shaidun Jehobah suna karfafa yaransu su sami ilimi sosai don su fahimci abubuwan da ke duniyar nan. Shaidun Jehobah da yawa suna da ilimin kimiyya da ya kunshi biochemistry (wato ilimin kimiyya da ke nazari a kan magungunan abubuwa masu rai) da fannin lissafi da kuma fannin ilimin halittu da kuma wasu abubuwa.
Yadda ’yan kimiyya suka kasa
Ba mu gaskata cewa ’yan kimiyya za su iya amsa dukan tambayoyin da mutane suke da su ba. a Alal misali, ’yan kimiyya da suke bincike game da ilimin sanin ma’adinai sun yin bincike don su san da mene ne aka halicci duniya, ban da haka ma, masu ilimin halittu suna bincike don su san yadda jikin mutum yake aiki. Amma me ya sa yin rayuwa ya dace da duniya, kuma me ya sa gabobin jikin mutum suke aiki a cikin jituwa?
Mun fahimci cewa Littafi Mai Tsarki ne kadai zai iya ba mu amsoshin da za su gamsar da mu. (Zabura 139:13-16; Ishaya 45:18) Saboda haka, mun gaskata cewa idan muna so mu sami ilimi muna bukatar mu rika nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma kimiyya.
A wasu lokuta, muna iya gani cewa an fadi wani abu a kimiyya da bai jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya fada ba. Amma wasu sabanin suna aukuwa ne saboda rashin fahimtar koyarwa Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Littafi Mai Tsarki bai koyar cewa an halicci duniyarmu a cikin ranaku shida na awoyi 24 ba.—Farawa 1:1; 2:4.
Sanannun ’yan kimiyya da kansu ba su yarda da wasu koyarwar kimiyya da ba a tabbatar da su ba. Alal misali, da yake duniya na cike da halittu, mun yarda da abin da wasu ‘yan kimiyya da kuma wasu suka yarda cewa halittu ba su bayyana hakan nan kawai da kansu ba.
a Wani likita a Austria da kuma wani mai suna Erwin Schrödinger da ya sami lambar yabo, sun rubuta cewa “kimiyya ba ta bayyana . . . dukan batutuwan da muke so mu sani.” Ban da wannan ma, Albert Einstein ya ce: “Misalai sun nuna mana cewa yin tunani kawai ba zai iya magance mana matsalolin rayuwa ba.”