Shaidun Jehobah Wani Sabon Addini Ne?
A’a, Shaidun Jehobah ba wani rukunin asiri ba ne. Mu Kiristoci ne da muke kokarin bin gurbin da Yesu Kristi ya bar mana kuma muna kokarin mu yi rayuwa daidai da koyarwarsa.
Mene ne Sabon Addini?
Ma’anar furucin nan ta bambanta wajen mutane da yawa. Amma ka lura da ra’ayi biyu game da abin da ake nufi da sabon addini kuma ka ga abin da ya sa hakan bai dace da mu ba.
Wasu sun ce furucin yana nufin wani addini ne dabam. Shaidun Jehobah ba wani sabon addini ba ne. Amma, muna bin tafarkin ibada da Kiristoci na karni na farko suka yi ne, wadanda misalinsu da koyarwarsu ke cikin Littafi Mai Tsarki. (2 Timotawus 3:16, 17) Mun yarda cewa ya kamata Nassosi Masu Tsarki ne su nuna mana tafarkin sujjada.
Wata ma’anar furucin kuma ita ce wani mugun rukuni ne na addini mai shugaba dan Adam. Shaidun Jehobah ba su da dan adam da ke shugabansu. Maimakon haka, muna bin ka’idar da Yesu ya tsara wa mabiyansa sa’ad da ya ce: ‘Gama daya ne Shugabanku, Kristi.’—Matta 23:10.
Shaidun Jehobah ba sabon addini ba ne amma addini ne da ke taimakon wadanda suke ciki da kuma mutanen yankin. Alal misali, hidimarmu ta taimaka wa mutane da yawa su daina wasu mugun hali, irin su shan kwaya da kuma buguwa da giya. Ban da haka, muna tsara azuzuwan koya karatu da rubutu kewaye da duniya da suke taimaka wa dubban mutane su iya karatu da rubutu. Muna kuma taimaka wa mutane a lokacin bala’i. Muna aiki sosai don mu taimaki wasu yadda Yesu ya umarci mabiyansa.—Matta 5:13-16.