Yaya Shaidun Jehobah Suke Amfani da Gudummawar da Suke Samu?
Muna amfani da gudummawar wajen yin ayyukan ibadarmu da kuma ba da agaji. Muna wadannan ayyukan ne don mu cim ma burinmu na musamman, wato taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu Kristi.—Matiyu 28:19, 20.
Ba ma amfani da gudummawar da ake bayarwa wajen sa wasu su yi arziki. Ba ma biyan dattawanmu kuma ba ma biyan wani a cikinmu don ya je wa’azi. Ba ma biyan wadanda suke hidima a ofisoshinmu da hedkwatarmu, har da wadanda suke hidima a matsayin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.
Irin Ayyukan da Muke Yi
Buga Littattafai: A kowace shekara, muna fassara Littafi Mai Tsarki da wasu littattafai da dama, muna buga su mu kuma rarraba wa mutane ba tare da mun ce su biya ba. Kari ga haka, muna saka littattafanmu a dandalin jw.org da kuma manhajar JW Library. Mutane ba sa biya kafin su yi amfani da dandalinmu ko manhajarmu kuma ba a saka talla a ciki don neman kudi.
Gine-gine da Yin Gyara: Muna gina da kuma kula da wuraren ibada a wurare da dama a duniya, don ’yan’uwanmu su sami wurare masu kyau don yin ibada. Haka ma muke yi da ofisoshinmu. ’Yan’uwanmu ne suke yin yawancin ayyukan nan da son ransu, hakan yana rage yawan kudin da muke kashewa.
Kula da Ayyukanmu: Gudummawar da ake bayarwa ne muke amfani da su wajen tafiyar da ayyukan da ake yi a hedkwatarmu, da ofisoshinmu, da kuma kula da wadanda suke kai ziyara a ikilisiyoyinmu.
Wa’azi: Ba a biyan Shaidun Jehobah don wa’azin da suke yi ko don su koya wa mutane “kalmar Allah.” (2 Korintiyawa 2:17) Amma kamar yadda Kiristoci a karni na farko suka yi, muna da wasu ’yan’uwa da aka zaba kuma aka koyar da su don yin wasu hidimomi. ’Yan’uwan nan suna amfani da yawancin lokacinsu wajen yin hidimomi da suka shafi aikin wa’azi kuma ana musu tanadin wurin kwana da abubuwan da suke bukata.—Filibiyawa 4:16, 17; 1 Timoti 5:17, 18.
Koyarwa: Gudummawar da ake bayarwa ne muke amfani da su wajen shirya manyan taron da muke yi. Kari ga haka, muna yin shirye-shirye da aka dauko daga Littafi Mai Tsarki da za a iya ji ko a kalla a bidiyo. Muna kuma da makarantu inda ake koyar da dattawa da wadanda suke yin hidima na cikakken lokaci don su iya yin hidimarsu da kyau.
Ba da Agaji: Muna samar da abinci da ruwan sha da wurin kwana ga wadanda bala’i ya shafa ko wadanda suke gudun hijira. Ba “’yan’uwanmu cikin Almasihu” ne kadai suke amfana daga ayyukan agajin nan ba, wadanda ba Shaidun Jehobah ba ma suna amfana.—Galatiyawa 6:10.