Ta Karfafa Mutane duk da Rashin Lafiyarta
Akwai wata Mashaidiyar Jehobah mai suna Clodean a Afirka ta Kudu. Ta yi rashin lafiya sosai da ya sa aka mata tiyata. Yanayinta ya yi tsanani kuma an bayyana mata jinya iri-iri aka ce ta zaba wanne za a mata. Kafin a mata tiyatar da ma bayan da aka mata tiyatar, Clodean ta yi famar zafin ciwon da kuma gajiya. Har kuma bayan da aka sallame ta a asibiti kuma ta koma gida, kwanciya take yi, ba ta iya zama. Annobar korona kuma ta sa ba dama mutane su rika zuwa gaisuwa.
Clodean ba ta so ta zauna tana bakin ciki don yanayin da ta sami kanta a ciki ba. Don haka, ta roki Allah ya taimake ta ita ma ta iya karfafa mutane. Da ta sami sauki har ta soma zama, nan da nan sai ta fara magana da ꞌyarꞌuwar makwabciyarta wadda ta taba nazarin Littafi Mai Tsarki, amma ta daina. Clodean ta mata waꞌazi. Abin da ta ji ya karfafa ta, har ta yarda a sake soma nazari da ita. Clodean ta bayyana mata yadda za ta amfana idan tana zuwa taro. Saꞌan nan ta taimaka mata ta iya shiga taron ikilisiyarsu da ake yi ta bidiyo. Matar kuwa ta shiga taron har ta daga hannu ta ba da amsa.
Clodean ta kuma tattauna da kanwar matar wadda ita ma ta so a yi nazari da ita. Har ta gaya ma Clodean sunayen wasu, da su ma za su so su ji waꞌazinmu. Yadda aka yi ke nan Clodean ta soma nazari da wasu mata hudu kuma. Amma ba shi ke nan ba!
Tsabar yadda Clodean ta so ta taimaka wa mutane, ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu mata guda goma, duk a wannan lokacin annobar. Dalibanta sun kama mata 16 ke nan. Wasunsu suna zuwa taro a kai a kai ta bidiyo. Da yake Clodean ta shagala wajen taimaka wa mutane, hakan ya sa ta rage damuwa a kan ciwon da ta ke yi. Kuma ta ce yadda Jehobah “Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya” ya karfafa ta, shi ne ya sa ita ma ta iya karfafa mutane.—2 Korintiyawa 1:3, 4.
Me daliban Clodean suka fada game da abubuwan da suka koya? Wata daga cikinsu ta ce: “Na amfana a hanyoyi da yawa. Abin da ya fi sa ni farin ciki shi ne sanin sunan Allah. Hakan ya sa na kusaci Jehobah sosai.” Mace na farko da Clodean ta yi mata waꞌazi kuma tana dokin yin baftisma nan ba da dadewa ba. Labaran matan nan suna sa Clodean farin ciki sosai. Yanzu Clodean ta warke daga ciwon da take yi.