Mun Yanke Shawarar Saukaka Rayuwarmu
Madián da Marcela wasu maꞌaurata masu kudi ne a lokacin da suke zama a birnin Medellín, a kasar Colombia. Ana biyan Madián albashi mai tsoka kuma sun zauna a wani babban gida. Amma wani abu ya faru da ya sa suka soma tunanin abin da ya kamata su saka farko a rayuwarsu. Maꞌauratan sun ce: “A 2006 muna halarci taron daꞌira na musamman mai jigo ‘Keep Your Eye Simple’. A cikin jawabai da yawa, an karfafa mu mu saukaka rayuwarmu don iya bauta wa Allah da dukan karfinmu. A karshen taron, mun gano cewa ba ma saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu. Mun saba da sayayya ko da ba mu da kudin biya a lokacin. Saboda haka, mukan ci bashi sosai.”
Jawabai da aka bayar a taron sun taimaka wa Madián da Marcela su fara saukaka rayuwarsu. Sun ce: “Mun daina kashe kudi barkatai. Mun koma karamin gida, mun sayar da motarmu kuma muka sayi babur.” Kari ga haka, sun daina zuwa wuraren kasuwancin da za su sa jarabar sayan kaya ya kama su. Sai suka kara amfani da lokacinsu suna waꞌazi kuma suka fara cudanya da ꞌyanꞌuwa da suke hidimar majagaba na musamman. a
Ba da dadewa ba sai Madián da Marcela sun yanke shawarar kaura zuwa wata karamar ikilisiya a wani kauye, inda ake bukatar masu shela sosai. Amma kafin su iya kaura, Madián ya yi murabus daga aikinsa. Ogarsa ta dauka cewa rashin tunani ne ke damun sa. Saboda haka, Madián ya tambaye ta ya ce: “Kina karban albashi mai yawa sosai, amma hakan yana sa ki farin ciki ne?” Ta yarda cewa a gaskiya ba ta farin ciki domin tana da matsaloli da yawa da ba ta iya magance su. Sai ya ce mata: “Abin da ya fi muhimmanci shi ne sanin abin da ke sa mutum farin ciki a rayuwa, ba kasancewa da kudi ba. Koya wa mutane abubuwa game da Allah yana sa ni da matata farin ciki, kuma muna so mu dada yin farin ciki. Shi ya sa muna so mu kara yawan lokacin da muke amfani da shi wajen yin wannan aikin.”
Madián da Marcela suna farin ciki kuma sun gamsu da rayuwarsu domin sun sa ibadarsu farko a rayuwarsu. Sun yi shekaru 13 yanzu suna yin hidima a ikilisiyoyin da ake bukatar masu shela a arewa maso yamman kasar Kolombiya.
a Reshen ofishin Shaidun Jehobah da ke kasa ne yake nada majagaba na musamman don su yi waꞌazi a wasu yankuna. Ana ba su karamin alawus don kula da kansu.