Allah Ya Amsa Adduꞌar Wata Makauniya
Wata Mashaidiya a Asiya mai suna Yanmei, ta taimaka ma wata makauniya mai suna Mingjie ta tsallake hanya. a Sai Mingjie ta ce mata: “Na gode. Allah ya yi miki albarka!” Bayan haka, sai Yanmei ta tambaye Mingjie ko za ta yarda su sake haduwa don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Daga baya, Mingjie ta ce ta dade tana adduꞌa kowace rana cewa Allah ya taimake ta ta sami addini na gaskiya. Me ya sa ta yi ta rokon Allah haka?
Mingjie ta bayyana cewa a 2008, wata abokiyarta ta gayyace ta zuwa wani cocin nakasassu kuma ta yarda ta bi ta. Da fādā ya gama waꞌazi sai Mingjie ta tambaye shi littafin da ya karanta musu. Fādān ya gaya mata cewa ya karanta musu Littafi Mai Tsarki ne, sahihiyar Kalmar Allah. Hakan ya sa Mingjie ta yi shaꞌawar karanta Littafi Mai Tsarki sosai. Saboda haka, ta sayi Littafi Mai Tsarki a yaren makafi na Caina kuma ta karanta shi a cikin watanni shida. Littafin ya kunshi kundi 32. Yayin da Mingjie take ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki, sai ta gano cewa koyarwar Allah-uku-cikin-daya da ake yi a cocinta, karya ce, kuma cewa Allah yana da suna, wato Jehobah.
A kwana a tashi, halin ꞌyan cocin ya sa Mingjie sanyin gwiwa. Ta ga cewa ba sa rayuwa bisa ga abin da take karantawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ꞌyan cocin suna ba mutanen da suke gani abinci mai kyau amma duk abin da ya rage ne ake ba makafi. Wannan rashin adalcin ya bata wa Mingjie rai sosai, saboda haka, ta soma neman wani coci da za ta rika halarta a yankinsu. Abin da ya sa Mingjie take adduꞌa ke nan don ta sami addini na gaskiya.
Alherin da Yanmei ta nuna wa Mingjie ya sa ta yarda Yanmei ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Daga baya, Mingjie ta halarci taro a karo na farko tare da Shaidun Jehobah. Mingjie ta tuna abin da ya faru kuma ta ce: “Ba zan taba mantawa da taro na farko da na halarta ba. ꞌYanꞌuwa sun marabce ni hannu bibbiyu kuma hakan ya ratsa zuciyata sosai. Ko da yake ni makauniya ce, na ga yadda ake nuna kauna ba tare da son kai ba.”
Mingjie ta soma ci gaba kuma ta soma halartar taro a kai a kai. Ta ji dadin rera wakokin Shaidun Jehobah sosai amma hakan bai yi mata sauki ba domin babu littafin wakar a yaren makafi da take karantawa. Saboda haka, ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar sun taimake ta ta wurin karanta mata kalmomin wakokin saꞌan nan ta zana su a yaren makafi da kanta. Ya dauke ta awoyi 22 ta zana duka wakokinmu 151 a cikin littafin! A Afrilu 2018, Mingjie ta fara yin waꞌazi tare da ikilisiyarta kuma daga baya takan yi awoyi 30 tana waꞌazi a kowane wata.
Yanmei ta taimaka wa Mingjie ta shirya don yin baftisma ta wajen daukan tambayoyi da kuma nassosi na littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will a sauti don Mingjie ta saurare su. A Yuli 2018, Mingjie ta yi baftisma. Ta ce: “Yadda ꞌyanꞌuwa maza da mata suka nuna mini kauna a wurin taron yankin ya ratsa zuciyata sosai. Hakan ya sa na zub da hawaye domin na ga cewa a yanzu, ina tare da mutanen Allah.” (Yohanna 13:34, 35) Yanzu, Mingjie ta kudura cewa za ta rika nuna kauna yadda aka nuna mata don haka ta soma hidimar mai waꞌazi na cikakken lokaci.
a An canja sunayen.