Faston Ya Sami Amsoshi
Wata rana, a lokacin da wata Mashaidiyar Jehobah mai suna Eliso take nazari da wata mata da take so ta san gaskiya, ba zato sai matan ta sami wasu baki. Wani Fasto ne da matarsa. Eliso ta ji cewa makonni biyu da suka wuce da tilo na wadannan ma’auratan ya yi ciwo kuma ya rasu.
Lokacin da Eliso take ta’azantar da su domin wannan rashin, sai faston da matarsa suka suma kuka sosai. Sai faston ya ce da fushi: “Ban gane dalilin da ya sa Allah ya bar irin wannan jarrabawar ya same mu ba! Yaya zai dauki da na tilo? Ina bauta masa shekaru 28. Ina abubuwa nagari kuma haka ne Allah zai sāka mini! Me ya sa Allah ya kashe dana?”
Sai Eliso ta bayyana ma ma’auratar cewa ba Allah ne ya daukin ran dansu ba. Ta kuma tattauna batutuwa kamar fansa, da tashin matattu da kuma dalilan da suka sa Allah ya bar mugayen abubuwa suke faruwa. Sai faston da matarsa suka gaya wa Eliso cewa yanzu ne ta ba su amsoshin tambayoyin da suke neman bayani a kansu.
A mako na gaba, sai faston da matarsa suka dawo kuma suka zauna tare da matar da ake nazari da ita. Eliso ta tattauna jigon “Bege na Gaskiya ga Kaunatattunka da Suka Mutu,” a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ma’auratar sun yi kalami sa’ad da suke tattaunawar.
Daga baya ma’auratar suka halarci taron yanki na musamman na Shaidun Jehobah a Tbilisi, a kasar Georgia. Kuma kauna ta gaskiya da hadin kai da suka gani a taron ya burge su sosai. Sun dade suna kokari su koya wa membobin cocin su wadannan halayen amma ba su yi nasara ba.