Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Na Daina Zalunci”

“Na Daina Zalunci”
  • Shekarar Haihuwa: 1956

  • Kasar Haihuwa: Kanada

  • Tarihi: Ina rayuwar lalata da zalunci kuma na fid ta rai

RAYUWATA A DĀ

 An haife ni a birnin Calgary da ke yankin Alberta a kasar Kanada. A lokacin da nake karami, iyayena sun kashe aure, kuma ni da mahaifiyata muka koma gidan iyayenta da zama. Iyayen mahaifiyata suna kaunar mu sosai kuma a lokacin ina farin ciki. Har yanzu ina tuna lokacin da nake farin ciki sa’ad da nake karami.

 A lokacin da nake dan shekara bakwai, rayuwata ta tabarbare sa’ad da mahaifiyata ta sake auran mahaifina kuma muka kaura zuwa birnin St. Louis da ke jihar Missouri a Amirka. Nan ba da dadewa ba, na gano cewa mahaifina mugu ne. Alal misali, a rana ta farko da na dawo daga sabuwar makarantar da aka saka ni, mahaifina ya ga cewa yaran makarantar sun ci zalina kuma ban rama ba. Ya yi fushi sosai kuma ya yi mini dūka fiye da wanda yaran suka yi mini! Hakan ya sa na soma fada da yara a makaranta sa’ad da nake dan shekara bakwai.

 Zafin halin mahaifina ya sa mahaifiyata bakin ciki sosai, kuma suna yawan fada. Na soma shan kwaya da giya sa’ad da nake shekara 11. Na zama mai saurin fushi sosai kuma a yawancin lokaci ina fada da mutane a kan titi. Na riga na zama azzalumi a lokacin da na kammala makarantar sakandare.

 Sa’ad da nake shekara 18, na shiga Sojan Ruwa na Amirka. A aikin, an koya mini yadda zan rika kashe mutane. Bayan shekara biyar, na bar aikin soja kuma na je makaranta don in yi nazarin halin ’yan Adam da fatan cewa hakan zai sa na sami aiki a Federal Bureau of Investigation wato Ofishin Bincike na Amirka. Na soma karatu a makarantar jami’a a Amirka kuma na ci gaba da yin hakan a Kanada sa’ad da na koma kasar.

 A makarantar jami’ar, na fid da rai cewa mutane za su gyara duniya. ’Yan Adam suna da son kai, kome a duniya banza ne kuma kamar babu mafita ga matsalolin da mutane ke fuskanta. Hakan ya sa na fid da rai cewa ’yan Adam za su iya sa duniyar nan ta gyaru.

 Da na ga kamar rayuwa ba ta da ma’ana, sai rayuwata ta dada tabarbarewa, abin da na mai da wa hankali shi ne shan giya da kwayoyi da neman kudi da kuma neman mata. Ina zuwa fati dabam-dabam kuma ina lalata da mata dabam-dabam. Da yake ni soja ne a dā, hakan ya ba ni ƙarfin zuciyar yin fada. Ina tunanin cewa ni ne zan tsai da abin da ya dace da wanda bai dace ba, kuma nakan yi fada da duk wanda na ga kamar yana cin zali wani. Amma hakan ya dada sa na zama azzalumi.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Wata rana sa’ad da ni da abokina muka sha kwaya muka bugu a gidansa kuma muke kokarin tura wiwi don a sayar, sai abokina ya tambaye ni ko na gaskata da Allah. Sai na ce, “Idan Allah ne yake jawo wahala a duniya, ba na so in san shi!” Washegari, a rana ta farko da na fara aiki, wani abokin aikina da Mashaidin Jehobah ne ya tambaye ni cewa: “Kana ganin cewa Allah ne yake jawo matsalolin da mutane ke fuskanta a duniya?” Wannan tambayar ta ba ni mamaki domin abin da na fada kafin wannan ranar ke nan, hakan ya sa na so in kara koya game da Allah. A cikin watanni shida, mun tattauna game da abubuwa da yawa kuma ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya amsa yawancin tambayoyin da na yi game da rayuwa.

 Budurwata da muke zama tare a lokacin, ba ta so in rika gaya mata abubuwan da nake koya. Wata ranar Lahadi, na gaya mata cewa Shaidun Jehobah za su zo gidanmu don yin nazari Littafi Mai Tsarki da mu. Washegari, da na dawo gida daga aiki, sai na ga cewa ta kwashe kome a gidan kuma ta tafi. Hakan ya sa na fita waje na yi kuka don bakin ciki. Na yi addu’a don Allah ya taimaka mini. Wannan shi ne lokaci na farko da na yi amfani da sunan Allah Jehobah a addu’ata.​—Zabura 83:18.

 Bayan kwana biyu, sai wasu ma’aurata Shaidun Jehobah suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni a lokaci na farko. Bayan sun tafi, na ci gaba da karanta littafin da muke nazarin da shi mai jigo Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya, na karance littafin gabaki daya a daren. * Abin da na koya game da Jehobah da kuma Dansa Yesu Kristi ya ratsa zuciyata sosai. Na koyi cewa Jehobah yana da tausayi kuma yana bakin ciki sa’ad da ya ga muna shan wahala. (Ishaya 63:9) Abu na musamman da ya fi ratsa zuciyata shi ne yadda Allah yake kauna ta da kuma hadayar da Dansa ya ba da domin ni. (1 Yohanna 4:10) Hakan ya sa na ga cewa Jehobah yana hakuri da ni domin “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (2 Bitrus 3:9) Kuma ya sa na san cewa Jehobah yana so in zama amininsa.​—Yohanna 6:44.

 A makon, na soma halartan taron Shaidun Jehobah. A lokacin, gashina yana da tsayi, ina sanye da dan kunne kuma shigar da na yi tana da ban tsoro, amma Shaidun sun marabce ni kamar danginsu da ya bata. Sun nuna cewa su Kiristoci na gaskiya ne. Na ji kamar na dawo gidan iyayen mahaifiyata, amma a wuri mafi kyau.

 Nan ba da dadewa ba, abubuwan da nake koya suka soma canja rayuwata. Na aske gashina, na daina lalatar da nake yi kuma na daina shan kwaya da giya. (1 Korintiyawa 6:​9, 10; 11:14) Ina so in faranta ran Jehobah. Don haka, da na koyi cewa Jehobah ya tsani wasu abubuwan da nake yi, ban ba da hujjar yin wadannan abubuwan ba kuma. A maimakon haka, na yi da-na-sani. Sai na cewa kaina, ‘Bai kamata ina yin wadannan abubuwan ba.’ Ba tare da bata lokaci ba sai na yi kokarin canja tunanina da ayyukana. Hakan ya sa na soma amfana daga bin ka’idodin Jehobah. Bayan watanni shida da soma nazarin Littafi Mai Tsarki, na yi baftisma a ranar 29 ga Yuli 1989.

YADDA NA AMFANA

 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in canja salon rayuwata. A dā, ina yawan fushi sa’ad da mutane suka bata mini rai. Amma yanzu ina yin iya kokarina don in yi “zaman lafiya da kowa.” (Romawa 12:18) Jehobah ne ya taimaka mini da Kalmarsa da kuma ruhunsa don in yi wadannan canje-canje kuma ina yi masa godiya.​—Galatiyawa 5:​22, 23; Ibraniyawa 4:12.

 Maimakon in rika shan kwayoyi da yin zalunci da kuma neman mata, yanzu ina kokari in faranta ran Jehobah kuma in yi iya kokarina a hidimarsa. Wasu shekaru bayan na yi baftisma, na kaura zuwa wata kasa don yin wa’azi a wurin da ake bukatar masu shela. Da shigewar lokaci, na koyar da mutane da yawa kuma na yi farin cikin ganin yadda Littafi Mai Tsarki ta sa suka canja salon rayuwarsu. Kari ga haka, ina farin ciki domin mahaifiyata ta zama Mashaidiyar Jehobah domin ta ga yadda na canja halina da kuma ayyukana.

 A kasar El Salvador, a shekara ta 1999 ne na sauke karatu daga makaratar da yanzu ake kira Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki. A makarantar, na koyi yadda zan rika yin ja-goranci a wa’azi da kuma yadda zan rika kula da ’yan’uwa a ikilisiya. Jim kadan bayan haka, sai na auri matata mai suna Eugenia. Kuma muna hidima ta cikakken lokaci tare a kasar Guatemala.

 A yanzu, maimakon na fid da rai, ina matukar farin ciki. Yin amfani da koyarwar Littafi Mai Tsarki ya sa na daina yin lalata da zalunci. Kuma ya sa ina rayuwa da farin ciki da salama.