Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Rayuwata Tana Ta Lalacewa

Rayuwata Tana Ta Lalacewa
  • Shekarar Haihuwa: 1971

  • Kasar Haihuwa: Tonga

  • Tarihi: Dan kwaya da aka daure a kurkuku

RAYUWATA A DĀ

 Mu ’yan kasar Tonga ne, kasa mai tsibirai wajen 170 da ke kudu maso yammacin Tekun Fasifik. Mu talakawa ne kuma ba mu da wutar lantarki ko mota. Amma muna da famfo a gidanmu kuma muna kiwon kaji kadan. Mahaifinmu yana da gonar ayaba da doya da gwaza da kuma rogo. A duk lokacin da muka sami hutu daga makaranta, ni da ’yan’uwana biyu mukan je mu taya shi yin aiki a gonar. Mahaifinmu yana ciyar da iyalinmu ta wajen sayar da amfanin gonar da kuma yin wasu kananan ayyuka. Muna daraja Littafi Mai Tsarki a iyalinmu kuma muna zuwa coci sosai kamar yadda mutane da yawa a tsibirinmu suke yi. Duk da haka, mun dauka cewa sai mun kaura zuwa wata kasa mai arziki ne za mu yi rayuwa mai inganci.

 Sa’ad da nake dan shekara 16, kawuna ya taimaka wa iyalinmu don mu kaura zuwa jihar California ta Amirka. Da muka isa wurin sai muka ga cewa al’adunmu sun bambanta sosai, kuma hakan bai zama mana da sauki ba. Ko da yake mun dan sami kudi, wurin da muka zauna unguwar talakawa ne kuma ana yawan fada da sayar da miyagun kwayoyi a wurin. Muna yawan jin harbe-harbe da dare, kuma yawancin mutane suna kwana cikin tsoro don ’yan bindiga. Mutane da yawa suna yawo da bindiga don su kāre kansu ko su raba gardama. An taba harbina a inda ake gardama, kuma har yau ina dauke da harsashin a kirjina.

 Da na shiga makarantar sakandare, sai na soma bin halin ’yan makarantarmu. Hakan ya sa da kadan da kadan na soma zuwa fatin ’yan iska, da shan giya, da cin zalin mutane, da kuma shan miyagun kwayoyi. Daga baya, na kamu da jarabar shan hodar iblis (cocaine). Sai na soma sata don in rika samun kudin da zan sayi miyagun kwayoyi. Duk da cewa mu a iyalinmu muna zuwa coci sosai, ba a koya min yadda zan guje halin banza ba. Sau da yawa an kama ni an kulle saboda fada. Rayuwata tana ta lalacewa kawai, har a karshe aka kai ni kurkuku.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Wata rana a 1997, sa’ad da nake kurkuku, wani da muke kurkukun tare ya gan ni rike da Littafi Mai Tsarki. Lokacin Kirsimati ne shi ya sa nake rike da Littafi Mai Tsarki. Yawancin mutanen Tonga suna daraja Kirsimati sosai. Sai mutumin ya tambaye ni ko na san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da haihuwar Yesu, ga shi kuma ban san kome game da hakan ba. Ya nuna min labarin a Littafi Mai Tsarki, kuma a wurin ne na gane cewa akwai abubuwa da yawa da ake yi a lokacin Kirsimati da ba a ambata su a Littafi Mai Tsarki ba. (Matiyu 2:​1-12; Luka 2:​5-14) Abin ya ba ni mamaki sosai kuma na soma tunani cewa kila akwai wasu abubuwa da dama a Littafi Mai Tsarki da ban sani ba. Ashe mutumin yana halartan taron Shaidun Jehobah da ake yi kowane mako a cikin kurkukun. Sai na yanke shawara cewa zan rika bin sa zuwa taron. Da na halarci taron, suna tattauna abin da ke littafin Ru’ya ta Yohanna ne. Ko da yake ban fahimci abin da ake fada sosai ba, na ga cewa duk abin da ake koyarwa daga Littafi Mai Tsarki ne.

 Da aka tambaye ni ko zan so a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, sai na yarda. Yin nazari da Shaidun Jehobah ya sa na gane cewa Allah ya yi alkawarin mayar da duniyar nan aljanna. (Ishaya 35:​5-8) Na kuma gane cewa idan ina so in faranta wa Allah rai, wajibi ne in yi wasu canje-canje a rayuwata. Kari ga haka, Allah ba zai bar ni in shiga aljanna ba idan na ci gaba da yin munanan abubuwan da nake yi. (1 Korintiyawa 6:​9, 10) Hakan ya sa na kudura cewa zan daina saurin fushi, in bar shan taba da miyagun kwayoyi, kuma in daina yin tilis da giya.

 Da na kusan fita daga kurkuku a shekara ta 1999, sai aka mayar da ni wani kurkuku dabam. Na yi fiye da shekara daya ban hadu da Shaidun Jehobah ba. Amma na ci gaba da yin canje-canje a rayuwata. A shekara ta 2000, gwamnatin Amirka ta janye ’yancin da aka ba ni na zama a kasar, kuma aka mayar da ni kasarmu Tonga.

 Da na koma Tonga, sai na nemi Shaidun Jehobah kuma na ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Na ji dadin abin da nake koya, kuma yadda suke amfani da Littafi Mai Tsarki ya burge ni don haka ne Shaidun Jehobah da na hadu da su a Amirka suke yi.

 Mahaifina sanannen mutum ne a garinmu don yana da babban matsayi a coci. Don haka, da farko iyalina ba su so yadda nake tarayya da Shaidun Jehobah ba. Amma a kwana a tashi, da suka ga yadda bin koyarwar Littafi Mai Tsarki yake gyara halina, hakan ya faranta musu rai.

Kowane sati nakan wuni ina shan kava, kamar yadda maza da yawa a Tonga suke yi

 Wani abin da ya min wuya in daina shi ne shan wani irin giyan da mutanenmu suke yi. Maza da yawa a Tonga sukan wuni suna shan giyar da ake kira kava, wanda ake yi da jijiyar wani irin barkono. Sai ni ma na soma zuwa wurin da ake sayar da kava kusan kowane dare, in yi ta sha har sai na bugu. Wani abin da ya jawo hakan shi ne, na soma harka da abokan da ba sa bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Daga baya, Shaidun Jehobah sun taimaka min in gane cewa irin halin nan yana bata wa Allah rai. Sai na canja halina don Allah ya amince da ni kuma in sami albarkarsa.

 Na soma halartan duka taron Shaidun Jehobah. Yin tarayya da mutanen da suke so su yi abin da Allah yake so ya taimaka min in daina halaye marasa kyau. A shekara ta 2002, na zama Mashaidin Jehobah sa’ad da na yi baftisma.

YADDA NA AMFANA

 Zan iya cewa Allah ya yi hakuri da ni kamar yadda aka ambata a Littafi Mai Tsarki cewa: “Ubangiji . . . hakuri yake yi da ku. Ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (2 Bitrus 3:⁠9) Da Allah ya so, da tuni ya halaka wannan duniyar, amma ya bar duniya ta kasance har yanzu don mutane kamar ni su tuba kuma su soma yin abin da zai faranta masa rai. Kuma na san cewa da taimakon Allah zan iya taimaka wa wasu su tuba.

 Da taimakon Jehobah, na daina rayuwar da za ta kai ni ga halaka. Yanzu ba na sata don in sayan kayan maye. A maimakon haka, ina kokari in taimaka wa makwabtana su ma su zama aminan Jehobah. Bayan na zama Mashaidin Jehobah ne na hadu da wata kyakkyawar mace mai suna Tea da na aura. Da ni da matata da danmu muna zaman lafiya. Kuma muna koya wa mutane abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da yadda mutane za su iya rayuwa har abada cikin salama a aljanna a nan gaba.