Koma ka ga abin da ke ciki

Abin da Muke Yi da Bayananka—Sifen

Abin da Muke Yi da Bayananka—Sifen

Idan mutum ya zama mai shela, ya amince da tsarin da kungiyar Jehobah a fadin duniya take bi. Zai fahimci cewa ikilisiyoyin Shaidun Jehobah da ofishin Shaidun Jehobah da kuma adireshin da Shaidun Jehobah suka yi rajista a kasashe suna amfani da bayaninsa yadda ya kamata don kungiyar ta samu ci gaba. Saboda haka, masu shela suna ba da bayanansu wa ikilisiyar da suke ciki kamar yadda yake a cikin littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will don su iya yin ibadarsu da kuma ayyukan ibada yadda ya kamata.—1 Bitrus 5:2.

Masu shela suna iya ba da karin bayani game da kansu ga Shaidun Jehobah don su iya sa hannu a wasu ayyuka na ibada. Hakan ya kunshi sunan mutumin da kwanan watan da aka haife shi da kuma ko shi namiji ne ko ta mace da kwanan watan da ya yi baftisma da inda yake zama da hidimar da yake yi da kuma matsayin da yake da shi a ikilisiyarsu. Abin da bayanin yake dauke da shi ya hada da abin da mai shelar ya yi imani da shi da kuma wasu bayanai na asiri. Muna tattara bayanan nan, da dauka a sauti, da tsara su da ajiye su, da kuma yin wasu ayyuka game da bayanan.

Dokar Tsare Bayanai a kasar nan:

Organic Law on the Protection of Personal Data and General Data Protection Regulation (EU) 2016/679.

Ta Dokar Tsare Bayanan nan, masu shela sun yarda ikilisiya ta yi amfani da bayanansu don wasu ayyuka na addini wadanda suka hada da:

  • halartan taro na ikilisiya da kuma wasu ayyuka da za a yi a ikilisiya;

  • ba wa mutumin wani aiki a taron ikilisiya ko na da’ira ko kuma taron yanki da ake dauka a sauti da Shaidun Jehobah a duk duniya suke saurara;

  • yin wasu ayyuka ko kuma hidima a cikin ikilisiya da za a bukaci sunan mutumin da kuma aikin da zai yi, wanda za a saka a kan allon nuna sanarwa da ke a Majami’un Mulki na Shaidun Jehobah;

  • kula da katin Rahoto na Mai Shela na Ikilisiya;

  • yin ziyara da kuma kulawa da dattawan ikilisiya suke yi (Ayyukan Manzanni 20:28; Yaƙub 5:14, 15);

  • cika wani bayani game da mutumin don a yi amfani da shi sa’ad da tsautsayi ya auku.

Za a ci gaba da adana bayanin nan muddin mutumin ya cika abubuwan da aka ambata a baya. Idan mai shela ya ki ya sa hannu a fom na Na Amince a Yi Amfani da Bayanina Na Sirri, ikilisiyar ba za ta iya ba wa mutumin wasu irin ayyuka ba ko kuma yarda masa ya yi wasu ayyuka na hidima ba.

Idan da bukata, za a iya aika bayanin nan zuwa duk wani adireshin da Shaidun Jehobah suka yi rajista. Masu shela su san cewa za a iya tura bayanansu zuwa wadannan adireshin da ke wasu kasashe da tsarin kāre bayanan mutane ya bambanta da na kasarsu. Amma, masu shela su san cewa wuraren da aka aika bayanansu har da hedkwatar Shaidun Jehobah da ke a Amirka za su bi Tsarin da Shaidun Jehobah Suke Bi Wajen Tsare Bayanansu.

Masu shela suna da damar su duba, su ce a share, su ce kada a yi amfani da bayaninsu ko kuma su yi wani gyara a cikin bayanan da suka bayar. Masu shela za su iya canja ra’ayinsu game da bayanan da suka bayar a duk lokacin da suke so. Idan mai shela ya ki a yi amfani da bayanin da ya bayar, bisa ga ’yancin da kungiyar Shaidun Jehobah take da shi a kan membobinta ko kuma bisa ga dokar da ke cikin Dokar Tsare Bayanai, Shaidun Jehobah za su iya ci gaba da yin amfani da bayanin mai shelan. Masu shela su sani cewa suna da damar su sanar wa kungiyar da ke kula da wadannan bayanan a kasarsu idan suna da wata matsala game da bayanansu.

Shaidun Jehobah suna daukan matakai da yawa don su iya tsare wadannan bayanan da suka yi daidai da Dokar Tsare Bayanai. Masu shela su sani cewa wadanda za su iya bincika bayanansu wadanda aka ba su izinin yin haka ne saboda abubuwan da aka ambata a baya.

Idan kana son karin bayani, ka tuntubi wannan adireshi ta imel:

DataProtectionOfficer.ES@jw.org.

Masu shela su san cewa za su iya ganin kungiyar da take kula da dokar tsare bayanai na kasarsu da wadanda suke wakiltar kungiyar idan akwai, da kuma wadanda suke kāre bayanan a shafin Masu Tsare Bayanai da ke jw.org/ha.

A kan iya samun wasu gyare-gyare a ayyukanmu na ibada, ko kuma a dokokin kasarmu da kuma tsarin na’ura da ake amfani da su. Idan ana bukatar yin gyara a shafin Yadda Muke Amfani da Bayanai, za a yi gyare-gyaren kuma a saka shi a shafin don masu shela su iya sanin bayanan da muke bukata da kuma yadda muke amfani su. Don Allah, ku dinga duba wannan shafin don ku ga gyarar da aka yi.