Koma ka ga abin da ke ciki

Tsarin da Shaidun Jehobah Suke Bi Wajen Tsare Bayananka

Tsarin da Shaidun Jehobah Suke Bi Wajen Tsare Bayananka

Kungiyar Jehobah a fadin duniya tana daraja ’yancin da mutane suke da shi da kuma ’yancin kāre bayanansu. Kungiyar tana tattaunawa da membobinta sosai da kuma karban bayanai game da su don ta iya taimaka musu idan da bukata kuma a samu ci gaba a ayyukan da kungiyar take yi. Kungiyar tana yin iya kokarinta don ta tsare batun asiri da kuma kāre bayanan mutane. (Karin Magana 15:22; 25:9) Kungiyar tana daukan batun asiri da muhimmanci sosai.—Karin Magana 20:19.

Kasashe da yawa sun kafa dokar tsare bayanai don su iya kāre bayanan mutane. An dade da sanin kungiyar Shaidun Jehobah da kuma ofisoshinsu da daukan batun asiri da muhimmanci sosai. Sun soma yin hakan tun kafin aka kafa dokar tsare bayanai. Kungiyar za ta ci gaba da amfani da tsarinta na kāre bayanai don ta tsare bayanan mutane.

Tsarin da Ake Bi Don Kāre Bayanai. Kungiyar tana amfani da wannan tsarin da aka ambata a kasa don ta kāre bayananka:

  1. Za mu yi amfani da bayananka a hanyar da doka ta amince da ita.

  2. Za mu karbi bayananka kuma mu yi amfani da su yadda ya kamata don ci gaban kungiyar.

  3. Za a adana bayananka kuma ba za a samu kuskure ba. Idan akwai kuskure, za mu gyara shi da zarar mun san da hakan.

  4. Za mu ci gaba da adana bayananka idan muna da bukatar yin hakan don amfanin kungiyar.

  5. Za a mai da hankali don kada a fallasa sirrinka.

  6. Muna iya kokari wajen hana wadanda ba su da izinin ganin bayanai don kada su ga bayananka. Duka kwamfutar da suke dauke da bayanan mutane suna da kalmar sirri na shiga, kuma hakan na nufin cewa wadanda suka san kalmar ne kawai za su iya shiga kwamfutar. Ana kulle ofisoshin bayan an tashi daga aiki kuma wadanda suke da izini ne kawai za su iya shiga.

  7. Ba za mu tura ma wasu ofisoshin da ke wasu kasashe bayananka ba, sai dai idan ta hakan ne za a iya cim ma abubuwan da ake so a yi a madadin kungiyar. Da zarar mutum ya zama mashaidin Jehobah, ya amince da wannan tsarin da yardar ransa.

Mu kafa wannan tsarin bisa ga abin da aka ce a littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will game da yadda ya kamata mu yi amfani da bayananka. Ana ba wa kowane mutum wannan littafin da zarar ya zama mai shela. Don samun karin bayanin, ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will.

Kungiyar ta ba wa kowane mutum ’yancin samu kariya a kan bayanansa da yin gyara ko goge bayanansa. An bayyana wannan batun a shafin nan Tsarin da Ake Bi Wajen Tsare Bayananka, a karkashin jigo nan ’Yancin da Kake da Shi.

Abubuwan da aka ambata a Tsarin da Shaidun Jehobah Suke Bi Wajen Tsare Bayananka sun nuna yadda Shaidun Jehobah a fadin duniya suke kāre bayananka.